Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa za ta soma cafke masu sayar da magungunan gargajiya da ke amfani da kalmomin batsa yayin tallata hajarsu.
Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dokta Usman Tijjani Aliyu ne ya bayyana hakan yayin zanta wa da manema labarai, inda ya ce gwamnatin ta kafa kwamitin da zai tankado keyar masu amfani da kalmomin batsa yayin tallata magungunan gargajiya a fadin jihar.
- Yaya kuke kallon farfasa rumbuna ajiya a wasu sassan Najeriya?
- COVID-19: Saudiyya za ta biya iyalan ma’ikatan da suka mutu diyya
Dokta Aliyu ya ce kwamitin wanda zai fara aiki nan take zai kasance karkashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa da kuma Hukumar KAROTA da ta ’Yan Hisba da sauran hukumomin Tsaro a matsayin mambobin kwamitin.
Ya ce jami’an KAROTA da na Hisbah gwamnatin ta dora wa nauyin kamen wadanda suka saba wa dokar a jihar tare da gurfanar da su a gaban kotun da ta dace.
Sakataren ya sanar cewa dabi’ar yin amfani da kalamai na batsa da masu tallata magungunan gargajiya ke yi a jihar ta kai munzali na intaha wanda kuma gwamnati ba za ta lamunta a ci gaba da yin hakan ba.