Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da sunan Dokta Yusuf Jibril JY a matsayin daya daga cikin mutum tara da za a yi wa mukamin Kwamishina a Jihar.
Jibril, ya kasance matashi mafi karancin shekaru daga cikin jerin sunayen wadanda za a nada mukamin sabbin Kwamishinoni a jihar.
- A gaggauta hukunta wadanda suka kashe Sheikh Aisami —JIBWIS
- za a samu mamakon ruwan sama da ambaliya ranakun Talata da Laraba a Pakistan – NDMA
Matashin mai shekaru 33 zai kasance irinsa na farko a Jihar Kano da za a yi wa mukamin Kwamishina.
Tuni Majalisar Dokokin Jihar, ta tantance Jibril tare sa wasu mutum takwas, wadanda za a yi wa mukamin Kwamishinoni.
Wannan na zuwa ne bayan ajiye aiki da wasu Kwamishinonin jihar suka yi gabanin shiga zaben fidda-gwani, don neman guraben yin takara a zaben 2023.
Jibril dan asalin garin Rurum ne da ke Karamar Hukumar Rano a Jihar Kano.
Jibril, ya yi karatu har zuwa matakin Digiri, wanda daga nan ne ya shiga harkar kasuwanci, inda ya ke kasuwancin dakon mai a karkashin kamfaninsa mai suna JY Global Services.
Nadin nasa a matsayinsa na matashi zai bude kofa ga matasa musamman wadanda ke rajin ganin an yi tafiya da su a gwamnatance don sharbar romon dimokuradiyya.
Tuni matasa a jihar suka shiga yaba wa Ganduje kan mika sunansa ga majalisar dokokin jihar don tantance shi, inda suke ganin an sanya kwarya a burminta.
Kungiyoyi masu zaman kansu a baya-bayan nan sun sha kiran gwamnatin Jihar da ta yi kokarin jan matasa a jiki don damawa da su.