Gwamnatin Jihar Kano ta umarci kafatanin ma’aikatanta da su koma bakin aiki bayan zaman gida da ce su yi a yunkurinta na dakile yaduwar annobar Coronavirus.
Sanarwar hakan ta fito ne a ranar Laraba daga bakin Kwamishinan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba.
- Rashin fada wa gwamnati gaskiya ne ya jefa Najeriya cikin rikici — Osinbajo
- Rashin tsaro: Babu wanda ya tsira a Najeriya —Dahiru Bauchi
Kwamishinan ya ce matakin hakan na zuwa ne a sakamakon nasarar da aka samu a yaki da annobar cutar Coronavirus a tsawon watannu ukun da suka gabata.
Malam Garba ya ce, dole ne shugabannin hukumomi da manyan jami’an gwamnati su tabbatar an kiyaye dokokin da gwamnati da mahukuntan lafiya suka shar’anta musu.
Ana iya tuna cewa, a watan Janairun da ya gabata ne gwamnatin jihar ta nemi ma’aikata su zauna a gida bayan da guguwar annobar cutar Coronavirus ta sake kadawa a zagaye na biyu.