Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya rattaba hannu kan sabon kudirin yi wa dokar masarautun Kano kwaskwarima wadda ta mayar da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar na dindindin.
Hakan na zuwa ne bayan yi wa dokar masarautun Kano kwaskwarima wadda a baya yayin da Tsohon Sarki Muhammadu Sanusu na biyu ke gadon sarauta, ta aminta da karba-karba na Shugabancin Majalisar a tsakanin Sarakunan Jihar biyar.
- Hadimin Ganduje ya yi magana ta farko bayan dakatar da shi
- Sakataren Masarautar Kano Mahmud Bayero ya rasu
Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Abba Anwar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoban 2020.
Sanarwar da hadimin Gwamnan ya fitar ta ce “an dakatar da kudirin karba-karba na Shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar, kuma a yanzu Sarki Aminu Ado Bayero ya zama shugabanta na dindindin.”
Haka kuma sanarwar ta ce “Gidan Shettima zai kasance babban zauren Majalisar Sarakunan wanda ‘yar gajeruwar tazara ke tsakaninsa da Fadar Sarkin Kano.”
Alhaji Abba ya ce “a yanzu sabuwar dokar ta aminta da Masu nadin sarki biyar daga kowace daya daga cikin Masarautun jihar biyar sabanin yadda ta kasance a baya inda masu nadin sarkin suka kasance hudu daga kowace masarauta.”
Ya kuma sanar cewa, za a rantsar da Shugaban Majalisar Sarakunan na ba da jimawa ba a gidan Shettima wanda a yanzu ake yi masa gyare-gyare.