Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa, Hakimin Kibiya, a matsayin sabon Sarkin Rano.
Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa ya cike gurbin da marigayi tsohon sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar ya bari bayan Allah Ya yi masa rasuwa a makon jiya.
tsohon sarkin Rano ya rasu ne cikin ‘yan awwani bayan an kwatar da shi a Asibiti,kuma zuwa wannan lokacin babu bayanin musababbin mutuwar sa.
Marigayin shine sarkin Rano na farko, bayan da gwamna Ganduje ya samar da karinmasarautu hudu masu daraja ta daya a jihar Kano.