✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya dauki nauyin karatun matashiyar da ya yi wa afuwa

Mutuniyar kirki ce don a gaskiya tun da ta zo ba a samu wata matsala da ita ba.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin daukar nauyin karatun wata matashiya da ya yi wa afuwa bayan da ta kwashe shekara bakwai a gidan yari sanadiyyar kashe mijinta da ta yi.

Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Daurarru da Gyaran halin ta Najeriya shiyyar Kano, DSP Misbahu Lawan ne ya bayyana hakan.

“Gwamna ya dauki alkawarin zai kula da iliminta da makamantansu, saboda shawarar da ita Hukumar Gidan Ajiya da Gyaran Hali ta bayar na cewa mutuniyar kirki ce.

“Don a gaskiya tun da ta zo ba a taba samun wata matsala da ita ba,” in ji shi.

A cewarsa, shekarun Rahma Hussain 13 da haihuwa kuma tana aji 3 na Makaranatar Firamare a lokacin da aka yi mata aure.

“Wannan kwamiti na Shugaban Kasa da suka zo suka kai ziyara ga mai girma gwamna, inda suka nemi gwamna da ya kalli wannan yarinya saboda an yi mata aure ne na dole kuma yarinya ce karama tana da buri a rayuwarta.

“AlhamdulilLahi gwamna ya yi mata afuwa aka kuma yafe mata,” a cewar Lawan.

Rahma Hussaini wacce a banan nan ne ta cika shekaru 20 daidai da haihuwa ta nanata godiya ga gwamnan Kano.

A cikin wani sauti da aka makala a cikin sanarwar, matar ta bayyana farin cikinta da sakin ta da aka yi, tare da godiya ga kwamitin da gwamnan da kuma jami’an gidan yari da suka nema mata mafita.

“Mai girma gwamna na gode, na gode Allah ya saka da alheri, Allah ya raba ka da kujerarka lafiya.

“Kuma na ji ka yi min alkawari da makaranta, Allah ya ba ka ikon iyawa, na gode Allah ya saka da alheri,” Ramha ta ce cikin hawaye.

A shekarar 2014 ne Babbar Kotun Kano ta yanke hukunci kisa ga Rahma bayan samun ta da laifin kashe mijinta ta hanyar soka masa wuka a cikin sa.

Bayanai sun ce ta daba wa mijinta wuka a Unguwar Darmanawa da ke Karamar Hukumar Tarauni, kasa da mako guda da auren su.

Sai dai Rahma Hussaini ta fada wa kotu a lokacin cewa, yi mata auren dole ne ya sanysa ta sokawa mijin nata wuka a ciki kuma ya mutu.

Bayan sauraron shari’ar kusan tsawon shekaru 4, a shekara ta 2018 ne Alkalin Kotun Mai Shari’a R.A Sadik ya yanke mata hukuncin kisa, amma tare da danka hurumin yi mata afuwa a hannun gwamna, la’akari da karancin shekarun ta da kuma yanayin tursasa mata auren dole.

Sai dai shekaru 3 bayan wannan hukunci, gwamnan na Kano ya amince da shawarwarin Kwamitin Shugaban Kasa kan yi wa daurarru afuwa da na Hukumomin Kula da Gidajen Daurarru na Kano, inda a Juma’ar da ta gaba Rahma Hussaini ta shaki iskar ’yanci.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamitin Shugaban Kasar a karkashin jagorancin Mai Shari’a Ishaq Bello, ya nema mata afuwa a ranar Juma’a tare da wasu fursunoni 30 da aka sako daga gidajen yari daban-daban na jihar.