Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya dakatar da hadiminsa na sadarwar zamani, Salihu Tanko Yakasai saboda wani sako sukar Shugaba Muhammadu Buhari kan sashen ‘yan sanda na SARS da ya wallafa.
Kwamishinan Labarai na Jihar, Malam Muhammadu Garba, yayin sanar da hakan ga manema labarai a ranar Lahadi ya hori jami’an gwamnati da su guji yin kalaman da ke iya jawo rudu ba gaira ba dalili.
Ya ce, “Duk da cewa hadimin gwamnan ya bayyana cewa kalaman nasa ra’ayinsa kashin kansa ne, yan da wuya a bambance hakan duba da matsinsa na jami’in gwamnati a kan al’amuran da suka shafi jama’a”.
Salihu wanda aka fi sani da Dawisu a shafukan zumunta ya soki Shugaba Muhammadu Buhari kan rashin yin komai a kan koken ‘yan Najeriya na game da jami’an sashen ‘yan sanda mai yaki da fashi da sauran manyan laifuka (SARS).
A sakon da ya wallafa a shafinsa na zumunta Salihu Tanko Yakasai ya soki manufofin Gwamnatin Tarayya, lamarin da ake ganin ya yi sanadiyyar dakatar da shi daga aiki.
Bayan zaben Gwamnan Jihar Edo wanda jam’iyyar APC ta fadi Salihu ya fara sukar Gwamnatin Buhari.
A sakon da ya wallafa a safiyar Lahadi, ranar da aka sanar da rushe SARS, Salihu ya ce, “Ban taba ganin gwamnatin da ba ta damu da abin da ya dami jama’a ba irin ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
“Sau da yawa idan mutane na cikin mawuyacin hali suna bukatar samun tabbacin daga gare shi cewa zai magance matsalar amma ba sa samu.
“Rashin kulawar ta yi yawa; Yi wa mutane magana game da abubuwan da ke damunsu ya koma sai ka ce wata alfarma kake musu.
“Sau tari ka kasa ware minti biyar ka lallashi jama’ar kasar da ka karade jihohi 36 kana rokon su zabe ba. Akwai ban takaici”.
Karo na biyu ke nan da Gwamna Ganduje ke sallamar ma’aikatansa saboda abin da suke wallafawa a shafukan zumunta na sukar gwamnatin Buhari ko hadiman shugaban kasar.
A watan Afrilun wannan shekara, gwamnan ya sallami kwamishinan ayyukan jihar, Mu’azu Magaji Dansarauniya.
Idan ba a manta ba, gwamnan ya sallami Dansarauniya ne kan kalaman da tsohon kwamishinan ya wallafa na sukar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari, jim kadan bayan rasuwarsa.