Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya biya wa daliban jihar Kano alawus na Naira miliyan 300 da ke karatu a jami’ar El-Razi ta birnin Khartoum a Sudan.
Kakakin gwamnatin jihar Kabiru Alhassan Rurum ne bayyana hakan a karshen mako ya kuma ce, ana saran wadanda aka biya kudin, jami’ar zata yaye su a watan Mayu 2019.
Rurum ya ce, akwai dalibai 31 da ke karatu a jami’ar wadanda duk ‘yan asalin jihar Kano ne, 28 na daliban na karatun likitanci yayin da sauran na karatun magunguna da dai sauransu.