✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya ba iyalan marigayi Udoji Naira miliyan 3

Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tallafawa iyalan tsohon dan kwallon Kano Pillars Marigayi Chinedu Udoji da Naira miliyan 3. Gwamnan ya…

Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tallafawa iyalan tsohon dan kwallon Kano Pillars Marigayi Chinedu Udoji da Naira miliyan 3.

Gwamnan ya bayar da tallafi ne a lokacin da tawagar kulob din Pillars da kuma matar marigayin suka kai masa ziyara a ranar Asabar 7 ga wannan wata da muke ciki a fadar gwamnatin jihar.

Marigayi Chinedu Udoji, daya ne daga cikin ’yan kwallon Kano Pillars, ya rasu ne a ranar 18 ga watan Fabrairun wannan shekara a birnin Kano a wani hadarin mota da ya rutsa da shi.

Gwamnan a yayin bayar da tallafin ga matar marigayin, ya jinjinawa marigayin ne a bisa namijin kokarin da ya yi wajen daukaka martabar kulob din Pillars a lokacin da yake raye. 

“Udoji dan wasa ne da kulob din Pillars zai dade yana kewarsa, kuma dan wasa ne da ya jajirce wajen ganin kulob din ya samu daukaka a dukkan wasannin da yake yi.  Don haka ina alfaharin tallafawa iyalansa da Naira miliyan 3,” inji Gwamna Ganduje.

Alhaji Ibrahim Galadima, Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ne ya jagoranci tawagar da ta hada da iyalan Marigayi Udoji a yayin kai wa Gwamnan ziyara.

A  jawabinsa yayin ziyarar, ya nemi ’yan kwallon Kano Pillars ne su yi kokarin lashe kofin gasar firimiya ta bana don karrama marigayi Udoji.

Marigayi Udoji, yana kwallo ne a bangaren baya (Defender), ya taba zama kyaftin a kulob din Enyimba na Aba kafin ya canza sheka zuwa kulob din Kano Pillars.  Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya biyu.