Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da tallafin naira miliyan 16 ga iyalan mutanen da suka mutu sakamakon fashewar kayayyakin hada bam a jihar a kwanan nan.
Sai da hukumomi a jihar sun ce lamarin ya faru be a sakamakon fashewar wata tukunyar gas a Unguwar Sabon Gari da ke Jihar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget
- Duk da kukan talauci talakawan Najeriya na kara kiran waya
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum tara tare da raunata wasu da dama.
Gwamna Ganduje ya bayyana bayar da gudunmawar tasa ne a bayan gayyatar iyalan wanda abun ya shafe a gidan gwamnatin jihar.
Ya ce tallafin wani yunkuri ne na taimako da kuma jajanta wa iyalan wadanda suka rasu a harin.
Ya ce an bai wa iyalan kowane mutum tara da suka rasa rayukansu Naira miliyan daya, sannan an baiwa mai cibiyar Afrika da gininsa ya rushe kyautar Naira miliyan biyu, shi kuma mai makarantar Winners, an ba shi Naira miliyan daya.
Ragowar mutum 10 da suka ji munanan raunuka, gwamnatin Jihar ta ba su kyautar N200,000, yayin da kuma wasu daga cikin da ba su samu raunuka masu muni ba aka ba su N100,000.