✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje na bukatar jami’ar Amurka ta nemi afuwarsa saboda ‘damfarar sa’ da matsayin Farfesa

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Jami’ar East Carolina dake kasar Amurka da ta nemi gafararsa

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bukaci Jami’ar East Carolina da ke kasar Amurka da ta nemi gafararsa bisa zargin yi masa ta leko ta koma da matsayin farfesa.

Jami’ar, wacce tun da farko gwamnatin jihar ta ce ta tabbatar wa da Ganduje matsayin a ranar Juma’a ta fito ta nesanta kanta da takardar nadin.

A wata wasika da Aminiya ta sami kwafinta wacce aka aike wa gwamnan, jami’ar ta ce wasikar nadin da daya daga cikin malamanta yaa turo wa gwamnan ya yi ne a radin kansa ba tare da sanin ta ba.

To sai dai a wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya fitar da yammacin Lahadi, Gwamnatin ta ce tana bukatar jami’ar ta nemi afuwarta cikin gaggawa tare da hukunta duk wanda ke da hannu a cikin lamarin.

“Mun yi matukar Allah-wadai da kurar da wannan nadi ya tayar, wanda yunkuri ne na bata sunan gwamnan da ma na al’ummar Jihar Kano baki daya”, inji sanarwar.

Gwamnatin ta kuma nuna takaici kan yadda wasikar ta ruwaito cewa shugabannin makarantar sun amince cewa an yi kuskure wajen turo wasikar da ke dauke da nadin tun da farko.

Tirka-tirkar na zuwa ne kasa da mako daya bayan Gwamna Ganduje ta bakin kakakinsa, Abba Anwar ya sanar da nadin nasa daga Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci Gaba ta Kasa da Kasa (ICITD) a matsayin babban malami kuma Farfesa a fannin shugabanci na zamani.

Anwar dai tun da farko ya ce jami’ar ta nada mai gidan nasa ne bayan ta gamsu da salon kamun ludayinsa wajen samar da ingantaccen shugabanci da raya kasa a Jihar Kano.