Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa harsashin gina wa Malamai gidaje 500 a unguwar Rafin Malam da Yola da ke Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.
Gwamnan wanda mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce yanzu haka an bai wa Ma’aikatar Muhalli umarnin samar da irin da za a dasa bishiyu a gurin da aka ware domin gina gidajen.
- Mutumin da ya siyar da dansa da matarsa ya shiga hannu
- Batanci: Tambuwal ya cire dokar hana fita a Sakkwato
Gwamnan ya ce an kuma bai wa masu kwangilar umarnin siyan kayayyakin aikin a hannun ’yan kasuwa domin bunkasa tattalin arzikin Jihar ta Kano.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Gwamnan Kano, Hassan Musa Fagge ya fitar ranar Juma’a.
A cewarsa, gidajen 500 na daga cikin guda 3,500 da gwamnatin za ta gina a Unguwar da ta ware domin malaman makaranta.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin za ta samar da wutar lantarki, da ruwan sha, da kuma tituna wanda kuma za su zo ne a farashi mai rahusa domin malamai da ma’aikata da sauran talakawan gari su siya.
“Wadannan gidajen za su taimaka wajen habaka tattalin arzikin jihar wajen sama wa matasa aikin yi, shi ya sa muka bai wa ’yan kwangilar umarnin siyan kayayyakin aikinsu duka a hannun ’yan kasuwarmu,” in ji Ganduje.
Ya kuma ce gwamnatin na fatan ’yan kwagilar za su kammala aikin a kan lokaci.
Kazalika, ya yi godiya ga Gwamnatin Tarayya bisa gudummawar da ta bayar na raya gine-ginen gidaje a Jihar Kano.