Wani taron sirri kan makomar siyasar Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike da dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya jefa Jam’iyar PDP cikin fargaba.
Wata majiya daga kungiyar yakin neman zaben Tinubu ta shaida wa Aminiya cewa, taron wanda ya samu halartar mutane biyu daga kowanne bangare ya yi albarka.
- DAGA LARABA: Yadda Rabon Gado Ke Neman Zama Tarihi
- Tuban Bello Turji ba zai gaskata ba sai ya ajiye makamai —Gwamnatin Zamfara
“Ganawar ta yi mana dadi kuma za a cigaba da gudanar da makamanciyarta tsakanin bangarorin biyu”, in ji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, wadanda suka halarci taron daga bangaren Tinubu sun hada Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, da na Ekiti Kayode Fayemi.
Daga bangaren Wike kuma akwai Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, da na Oyo Seyi Makinde.
Rahotanni dai na nuna cewa ana kokarin cim-ma matsaya ne kan ko Wike zai dawo APC, ko kuma zai yiwa Tinubu aiki daga jam’iyyarsa ta PDP a zaben shugaban kasa na 2023.
Wani tsohon minista da ke tsagin Gwamna Wike ya ce bai ga abin tada jijiyar wuya don Wike da Tinubu sun yi taron ba, domin shi ma dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar na yin makamancinsa da gwamnonin APC.
Yunkurin ji ta bakin Festus Keyamo, kakakin tawagar yakin neman zaben dan takarar APC, da kuma Daraktan yada labarai Bayo Onanuga, da kakakin Tinubun Tunde Rahman ya ci tura, domin ba su amsa kira da sakonnin da muka tura musu ba.
A hannu guda kuma kakakin Atiku, Paul Ibe ya ki cewa komai kan lamarin.
Tun a baya dai tsohon ministan ayyuka, kuma jigo a Jam’iyyar APC, Sanata Adeseye Ogunlewe, ya shawarci Wike da ya koma wajen Tinubun, bisa zargin watsi da shi a siyasance da PDP ta yi.