✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Game da watsi da injunan sarrafa amfanin gona

Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da wasu injinan sarrafa amfanin gona na biliyoyin naira wadanda Ma’aikatar Harkokin Aikin Gona ta…

Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da wasu injinan sarrafa amfanin gona na biliyoyin naira wadanda Ma’aikatar Harkokin Aikin Gona ta Tarayya ta shigo da su a tsakanin 2012 zuwa 2014. Kuma wannan kadan ne daga cikin dubban misalan da za a buga game da barnata dukiyar al’ummar kasar nan.

Injina da na’urorin za a iya yin amfani da su ne wajen sarrafa kayan abinci irin su gero da dawa da masara da kuma alkama, sannan kuma da samar da fulawar garin rogo. Kamar yadda rahotannin suka tabbatar, an yi odar injinan ne musamman don rarraba su ga kungiyoyin kananan manoma a dukkan yankunan nan shida na Najeriya, amma abin takaici an yi watsi da su a filin Allah, inda ruwa da zafin rana ke cigaba da daidaita su a garin Kwali da ke Babban Birnin Tarayya Abuja tsawon shekaru.

Injinan wadanda tsohon Ministan Harkokin Noma kuma shugaban Babban Bankin Noma na Afirka na yanzu (ADB), Mista Akinwunmi Adesina ya sayo su a kan kudi kimanin Yuro miliyan biyar kimanin Naira biliyan biyu ke nan, daga wani kamfanin Turai mai suna ‘Compact Milling System’ a lokacin da yake kan kujerar ministan gona. Haka kuma an ruwaito cewa Ministan Ayyukan Gona da Raya Karkara ya kafa kwamitin bincike bayan da ya samu labarin yin watsi da injinan.    

Koda yake an yi zaton cewa ministan gonan, Cif Audu Ogbeh wanda yake jajirtacce akan sha’anin noma zai aiwatar da abinda ya dace, sannan ya gaggauta mika injinan ga wadanda suka cancance su. Bai kamata ya tsaya kafa kwamiti ko jiran rahotansa wanda kila ya shafe makonni bai mika sakamakon nasa ba, alhalin injinan na ci gaba da lalacewa. Bisa ga irin azamar da wannan gwamnatin ke da ita game da harkokin noma a Najeriya, ko kadan ba a tsammaci faruwar irin wannan tafiyar hawainiyar ba.    

Koda yake lamarin ya faru ne a zamanin gwamnatin da ta gabata, amma duk da haka babu wanda zai yi zaton cewa Ministan Buhari zai zuba ido ba tare da daukar matakin gaggawa ba har tsawon fiye shekaru biyu da shigar sa ofis, a yayin da kayayyakin ke ci gaba da lalacewa. Hakika abu ne sananne cewa dukkan jami’an gwamnati na alfahari tare kuma da samun tagomashi mai yawa daga ayyukan cigaban da gwamnati ta samar a lokacinsu, musamman a wannan fanni na noma.

A sarari yake cewa samar da dukkan na’urori da injinan sarrafa amfanin gona bai tsaya ga nasarorin gwamnati kawai ba, nasara ce ta dukkan kananan manoman da aka baiwa don kara wa abin suke nomawa armashi. Haka kuma zai rage tulin matsalolin da noman nasu ke fuskanta tsawon shekaru, sannan su zama manyan masu sarrafa amfanin da suka samar su da kansu, baya ga samar da ayyukan yi ga dubban al’umma. Amma fa irin wannan yin watsi da wancakalar da na’urori masu amfani, ba bakon abu ba ne a kasar nan, koda kuwa ran al’umma zai baci a yayin da suka gano irin halin ha’ula’in da wadannan kayayyakin na gwamnati suke ciki. 

Wadannan abubuwa na ci gaba da faruwa sakamakon siyasa da kuma rashawa, kuma babu mai daukar alhakin hakan, sannan koda ma an samu wani da laifin, ba hukunta shi ake yi ba, wannan ya sa sakarcin ya kara samu gindin zama. Haka fa kudaden al’umma ke salwanta a banza, sannan kyawawan tsare-tsare na kara zama abin kyama a kasar nan.  

Don haka lokaci ya yi da mutane za su rika daukar alhakin ayyukansu, sannan duk wanda aka samu da laifin aikata ba daidai ba ya dandana kudarsa. Sam bai dace a rika yin ko-oho da kayayyakin gwamnati ba, don kawai ba mallakar wani mutum guda ba. Wannan kaya fa mallakin dukkan al’umma ne, don haka wajibi a tsare tare da bada kariya ga dukkan kayayyakin al’umma. 

Idan da ace wani kamfanin da ba na gwamnati ba ne ya shigo da kayayyakin a misali, ba za a taba yin watsi da su ta irin wannan hanyar ba. Yawancin wadanda ke yin watsi da kayayyakin gwamnati suna gudanar da kayayyakin kasuwanci da harkokin kansu bisa kula ba tare da almubazzaranci ba. Amma game da kayan gwamnati sai labarin ya canja. 

E, lallai daga tsarin ne, amma ya kamata mu fara tunanin gyara tun yanzu. Bai kamata mu rika kafa hujja da cewa ‘salon Najeriya’ ba, wadda abin kunya ne matuka da kuma faduwar kimarmu baki daya, ba wai kawai ga shugabanni ba. 

A yayin da wannan rahoto ya gano wadannan injina da na’urorin da aka yi watsi da su a ma’aikatar aikin gona, mu na sane da cewa irin wadannan almubazzarancin na nan birjik a yawancin ma’aikatun gwamnati a dukkan matakai. Akwai kayayyakin gwamnati na makudan kudi da suka shafi lafiya da ilimi da sana’o’i da kuma fannin gona rututu a sassan kasar nan an yi watsi da su saboda rashin tsari da hange. 

Ya kamata gwamnati ta farka wajen like dukkan kafofin barna tare da gudanar da bincike kan ma’aikatu da sauran ofisoshin gwamnati don bankado irin wadannan kayayyaki da aka yi watsi da su wadanda za su iya taimakawa cigaban kasar nan. Wannan batu na injinan sarrafa amfanin gonan da aka yi watsi da su fa daya daga cikin dubu a farfajiyar ma’aikatun gwamnatin kasar nan.