An cigaba da kwantar da dan kwallon gaba na Kano Pillars a asibitin Murtala da ke Kano bayan an sallame shi a wani asibiti da ke Fatakwal a ranar Talatar da ta wuce bayan ya yi arangama da dan kwallon Ribers United a gasar rukunin firimiya da suka yi a garin Fatakwal.
A daidai minti takwas da fara wasa ne al’amarin ya faru a lokacin da ’yan kwallon biyu suka yi arangama da kai a kokarin dauke kwallo a sama. Hakan ta sa aka canja Gambo Mohammed a daidai minti 8 da fara wasa. Sai dai dan kwallon bai farfado ba sai da aka garzaya da shi asibitin Braithwaite Memorial Hospital da ke garin Fatakwal don duba lafiyarsa.
Ya zuwa ranar Talatar da ta wuce ne aka koma da dan kwallon Kano inda ya cigaba da kwanciya a asibitin Murtala don cigaba da samun kulawa.
A wata tattaunawa da jaridar Aminiya ta yi da Likitan da ke kula da ’yan kwallon Pillars, Idris Malikawa ya nuna Gambo Mohammed zai shafe makwanni yana jinya ba tare da ya buga musu kwallo ba.
“Wannan babban al’amari ne, kuma Allah Ya takaita da abin ya fi haka muni”, inji Malikawa.
Rahotanni sun nuna Gambo Mohammed ya yi arangama ne da dan kwallon Ribers United mai suna Wilson Andoh.
Idan za a tuna a bara Gambo Mohammed yana daga cikin ‘yan kwallon Pillars da suka samu rauni bayan barayi sun tare su da rana tsaka a wani gari da ke kusa da Abuja a kan hanyarsu ta zuwa Kudanci don yin wasa.
Gambo Mohammed zai yi jinyar makonni
An cigaba da kwantar da dan kwallon gaba na Kano Pillars a asibitin Murtala da ke Kano bayan an sallame shi a wani asibiti da…