✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gambiya: Shugaba Adama Barrow ya sake lashe zabe

Jam'iyyun adawa sun yi fatali da sakamakon zaben wanda Shugaba Barrow ya lashe da kashi 53 na kuri'un da aka jefa

Shugaban Kasar Gambiya, Adama Barrow ya lashe da gagarumar nasara domin fara wa’adin mulkinsa na biyu.

Hukumar zaben kasar ta sanar cewa Shugaba Barrow ya samu kuri’a 457,519 a yayin da babban abokin karawarsa, Ousainou Darboe, ya samu 238, 253.

Barrow ya yi nasara ne bayan ya samu kashi 53 cikin 100 na kuri’un da aka jefa a zaben da aka gudanar a ranar Asabar.

Sai dai kuma Darboe, wanda ya samu kashi 28 cikin 100 na kuri’un da wasu ’yan takara biyu, Mama Kandeh da Essa Mbye Faal, sun ki amincewa da sakamakon zaben.

“Akwai abin damuwa game da jinkirin da aka samu wajen bayyana sakomakon zaben sannan wakilan jam’iyyunmu na da korafi a kan wasu abubuwa da aka yi a wasu rumfunan zabe” inji sanarwar hadin gwiwar da suka fitar bayan sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi da dare.

Birnin Banjul ya kasance cikin kwanciyar hankali, ko da yake an girke ’yan sanda da motocin ruwan zafi a hedikwatar hukumar zaben da ke birnin.

Ana dai kallon zaben a matsayin zakaran gwajin dafin ci gaban tsarin dimokuradiyya da ta bambanta da lokacin mulkin tsohon shugaban kasar, Yahya Jammeh.

 

A wa’adin Shugaba Barrow na farko, tattalin arzikin kasar Gambiya ya samu koma baya sakamakon bullar cutar COVID-19, wadda ta kawo cikas ga hanyoyin samun kudaden shigar kasar.

Kasar ta dogara ne da bangaren yawon bude ido da kuma fitar da kifi da gyada zuwa wasu kasashe domin samun kudaden shiga.