A ranar Lahadin da ta gabata ce aka kammala gasar wasan kwallon kafar zaman lafiya a tsakanin al’ummomin Jihar Kano wanda kungiyar ICEDA ta dauki nauyin shirya shi.
Kimanin kungiyoyi 16 ne wadanda suka fito daga kananan hukumomi 11 da ke fadin Jihar Kano suka fafata a wannan gasa wacce aka yi kimanin wasanni 71 kafin a karshe a fitar da gwarzon wasa.
A farkon wasan da aka yi tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Gama Merite da kuma takwararta ta Kumbotso, an tashi babu ci wato ziro-ziro, wanda hakan ya bayar da dama aka gudanar da bugun daga kai sai mai tsaron gida inda kungiyar Gama ta lallasa takwararta ta Kumbotso da ci hudu da biyu.
Aminiya ta rawaito cewa dukkanin kungiyoyin wasan kwallon kafar sun karbi kofunan samun nasara a matsayin na daya da na biyu.
A tataunawarsa da Aminiya Shugaban kulob din Gama Merite Muhammad Rabi’u Mai garin Gama ya bayyana jin dadinsa da wanann nasara da suka samu tare da yaba wa wadanda suka shirya gasar. “A tsawon shekarun da na yi ina yin wasa tun ina matsayin dan wasa ban taba shiga wata gasar wasa mai tsari kamar wannan ba”.
Da yake jawabi tun da farko game da makasudin shirya gasar, Farfesa Muhammad Bello Shitu Malami a sashen Ilimin Manya da Ayyukan al’umma “Adult Education and Community Serbices” a Jami’ar Bayero da ke Kano wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar ICEDA ya bayyana cewa an shirya gasar ce don kara kulla zumunci tare da samar da hadin kai a tsakanin al’umma ta hanyar yin amfani da matasa wadanda ke da muhimmanci a tsarin ci gaban al’umma.
“Mun gano cewa matasa suna da babbar gudummawa da za su bayar wajen tabbatar da ci gaban al’umma. Haka kuma mun fuskanci yadda matasan suka mayar da hankalinsu ga harkar kwallon kafa ya sa muka zabi wannan hanya wajen cusa musu akidar hadin kai a junansu yadda za su taimaki al’ummomin yankunansu”
Farfesa M. B. Shitu ya kara da cewa “Abin da muke so cimmawa a karshe shi ne mu yi amfani da wadannan matasa da suke yin kwallo ta yadda za su bayar da gudummawa wajen ci gaban al’ummominsu musamman ta bangaren wanzar da zaman lafiya da kuma yin ayyuka na ci gaban al’umma.