✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gadar Kano zuwa Bauchi da ta shekara a karye ta zama tarkon mutuwa

Mutanen yanjin sun koma amfani da kwalekwale

  • ‘Daga farkon damina zuwa yanzu sama da mutum 20 sun mutu’
  • Tafiyar minti 15 ta koma ta minti 40 — Fasinjoji
  • ‘Da kwalekwale ake ketarewa da matafiya’

Sama da shekara daya ke nan da wata muhimmiyar gada da ke kan hanyar da take hada jihohin Kano da Jigawa da ta wuce zuwa wasu jihohin Arewa maso Gabas ta karye, kuma har yanzu gyaranta na neman gagara.

Gadar, wacce take garin Bakin Gada a karamar Hukumar Takai a Jihar Kano na iyakar Kano da Jigawa ce, a kan babbar hanyar da ake bi daga Kano zuwa Bauchi da Gombe da Taraba da wasu jihohi da dama.

Sai dai tun sama da shekara daya da karyewarta, kuma duk da muhimmancin hanyar ga harkar sufuri da habakar tattalin arziki, har yanzu an kasa kammala gyaranta.

Lamarin ya tilasta wa matafiya yin zagaye ta Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, su zagayo ta Birnin Kudu, sannan su dora da tafiyar.

Tafiya ce da ba ta wuce ta minti 15 zuwa 20 ba, amma matsalar gadar ta tilasta wa matafiya shafe sama da minti 40 wajen yin zagaye.

A wata ziyarar da Aminiya ta kai bakin gadar, ta iske cincirindon fasinjoji wadanda bin hanyar ya zamar musu dole suna ta kokarin sauka daga motoci da babura don hawa kwalekwale su tsallaka kogin, daga bisani su sake hawa wasu ababen hawan don ci gaba da tafiya.

‘Ana samun asarar rayuka sanadin kifewar kwalekwale’

A zantawarsa da wakilinmu, daya daga cikin fasinjojin da Aminiya ta tarar ya sauka daga wani kwalekwale, mai suna Surajo Maitama Kachako, ya ce ko a makon jiya wasu mutane sun nutse a kokarin tsallaka rafin, kuma har yanzu ana ta neman gawarwakinsu.

Yadda ake tsallakar da fasinjoji a karyayyar gadar
Yadda ake tsallakar da fasinjoji a karyayyar gadar

Ya ce, “Karyewar gadar ta haifar mana da matsaloli da dama. Wurin da a da muke biyan Naira 200, yanzu ya koma Naira 400 zuwa Naira 500.

“Amma a cikin haka, a kan samu matsala idan kogi ya kawo, ruwa ya yi ambaliya, saboda wasu ba su iya ruwa ba. Ko a irin haka wasu sun fada a ciki, su bace wasu ma ko labarinsu ba a samu.

“Ni kaina kanena, Abbas, yau kwana bakwai ke nan ba mu gan shi ba, ba mu san inda gawarsa take ba. Ba mu ga gawarwakinsu ba. Saboda haka muke rokon gwamnati ta duba halin da muke ciki,” inji shi.

Shi ma wani fasinja da Aminiya ta zanta da shi, Abdurrahman Sulaiman Warwadi, ya ce karyewar gadar ta jefa su a cikin kuncin rayuwa.

Ya ce a makon jiya wajen mutum hudu suka rasu a kogin.

A cewarsa, “Kafin faduwar damina, muna samu mu tsallaka da babura, amma lokacin da ruwa ya fara sauka, sai kamfanin suka zo suka karasa rusa ragowar gadar baki daya da nufin yin aikinta, amma kuma ga shi sun yi watsi da aikin.

“Shi ya sa a yanzu ba mu da zabi sai na bin wadannan kwalekwale duk da hadarin da suke da shi ga rayuwarmu,” inji shi.

‘Kudin mota ya ninka saboda zagayen da ake yi’

Shi kuwa Adamu Munkaila, wani matashi mai yi wa kasa hidima a garin Huguma, ya ce tunda gadar ta samu matsala, kudin da yake kashewa wajen sufuri suka ninka.

Ya ce, “Yanzu idan na fito daga Birnin Kudu, ya kamata a ce mun bi ta garin Baranda kamar yadda muka saba, mu bi ta Dutse, Kwanar Huguma sannan mu bi ta Takai, amma yanzu abin ya zama wahala, sai mun bi ta Dutse, mu bi ta Kiyawa, sannan mu je Takai.

Yadda masu kwalekwale ke tsallakar da fasinjoji
Yadda masu kwalekwale ke tsallakar da fasinjoji

“Kafin gadar ta karye, tafiyar ba ta fin minti 15 zuwa 20, amma yanzu nakan yi minti kusan 40, sannan kafin na samu mota ma nakan sha matukar wahala.

Akasarin direbobi sun hakura da bi ta wannan hanyar,” inji shi.

Adamu, ya ce a baya abin da yake biya ba ya wuce Naira 200 zuwa Naira 250 daga Birnin Kudu zuwa Kwanar Huguma, amma yanzu sakamakon zagayen, daga Birnin Kudu zuwa Dutse ma sai ya biya Naira 350, sannan daga Dutse kuma sai ya biya kamar Naira 150.

Ya ce a duk lokacin da suka hau kwalekwalen aka tsallakar da su, sukan biya Naira 50.

Duk da abin da muke samu, ba ma farin ciki da matsalar – Masu kwalekwale

Sai dai duk da a iya cewa masu tsallakar da mutane ta hanyar amfani da kwalekwalen gaba ta kai su, amma sun ce ba farin ciki suke yi da matsalar ba, saboda ’yan uwansu take shafa.

A cewar daya daga cikin masu tsallakar da mutanen, Abdullahi Inuwa, “Duk abin da za mu samu, ba son sa muke yi ba, mun fi son a gyara ta, domin daga farkon daminar nan, sama da mutum 20 sun rasu a nan.

“Mutane da yawa suna mutuwa. Yanzu haka ga wasu jiragen namu can an ajiye su an tafi neman gawarwaki. Jirgi ne ya kife da su. Idan aka yi ruwan sama ya yi ambaliya, kuma wasu ba su iya ninkaya ba ne ake samu matsalar.

“Muna rokon gwamnati ta taimaka ta kawo mana dauki ta hanyar gyara wannan gada domin ’yan uwanmu su daina mutuwa,” inji shi.

Na hakura da daukar fasinjan Kano zuwa Bauchi – Direba

Idris Haruna, wani direba dan asalin Jihar Kano da ya ce a baya yakan dauki fasinja daga Kano zuwa Bauchi, ya ce a yanzu ya hakura saboda karyewar gadar.

Yadda ake tsallakar da fasinjoji kafin su hau mota
Yadda ake tsallakar da fasinjoji kafin su hau mota

Ya ce, “Kafin faduwar damina, ana dan bude gadar mu tsallaka mu da masu babura, amma tunda aka barke ta sai dai ta kwalekwale, shi ma wasu suna tsoron hawan sa.

“Yanzu idan muka dauki fasinja zuwa Bauchi daga Kano, sai dai mu ajiye su a bakin gada su tsallaka ta kwalekwale, sannan su hau wata ta kai su.

“Hakan ya sa dole sai an yi musu juye sannan ga karin farashi. Masu jigilar kayan abinci kamar buhuna kuma suna fargabar tsallakawa, saboda tsoron kada sai an je tsakiyar ruwa kwalekwale ya kife da su,” inji shi.

Kamfanin da ke aikin gadar ya kwashe kayansa

Da Aminiya ta nemi jin ta bakin kamfanin da aka ba kwangilar aikin sake gina gadar, ta iske wajen da ya killace a kusa da gadar babu komai, in ban da wasu dakunan ma’aikata na wucin-gadi.

Da ta tambayi wasu masu gadi a wajen, sun shaida mata cewa tun kusan wata guda ke nan kamfanin ya kwashe komatsensa ya bar wajen.