Akalla mutum 936 ne aka tabbatar sun rasu a sakamakon hatsarin kwalekwale a cikin shekara uku da rabi da suka wuce a Najeriya.
Ganin yadda kasar ke ta asarar al’ummarta ta haka ne Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin waɗanda suka faru a baya-bayan nan, da nufin yi wa tufkar hanci.
Masana kuma sun shawarci gwamnatocin jihohi da na tarayya su ɗauki matakai a aikace, su samar da kwalekwalen zamani a yankunan da ake da buƙatar su, ba su tsaya yin magana a takarda ko yin ta’aziyya kawai ba.
- Majalisar Kano ta dakatar da Shugaban Hukumar Gwale kan sayar da filaye
- Yaron mota ya mutun bayan fadowa daga saman tirela tana gudu a Legas
Masanan sun bayyana wa Aminiya ainihin dalilan haɗɗuran da ake samu, da kuma hanyoyin da za a magance su, idan ana so.
Aminiya ta gano Allah Ya hore wa Najeriya ruwa na cikin gida mai tsawon kilomita 10,000 da ke ratsawa ta jihohi 28; kuma ƙasar na asarar rayuka a sanadiyyar sufurin ruwa, sakamkon rashin nagartattun dokoki, matakai da kuma kayan aiki.
Hakan ya sa aka bar ɓangaren a hannun mazauna karkara marasa ƙwarewar zamani wajen gudanar da wannan harka.
Hatsarin jirgin ruwa
Kimanin mako guda ke nan da gomman mutane suka rasa ta wannan hanya, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce kan halin ko-in-kula da gwamnati take nunawa ga ɓangaren sufurin ruwa na cikin gida, musamman a Arewacin kasar nan da ke da roguna da tafkuna.
A ranar 4 ga watan nan na Satumba, 2023, wani hatsarin kwalekwale ya yi ajalin mutun biyu daga cikin fasinjojiin da ya ɗauko daga yankin Mayo-Ine zuwa Mayo Belwa a Karamar Hukumar Belwa a Jihar Adamawa.
Bayan kwana huɗu kuma wani hatsarin a Tafkin Njuwa ya yi ajalin mutun 15 daga cikin fasinjoji 23 da ya dauko daga kauyen Rugange zuwa Karamar Hukumar Yola ta Kudu.
Kwana uku da suka wuce kuma hatsarin kwalekwale ya lakume rayukan manoma 30 a Karamar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja.
A ranar Litin kuma, wani ya auku a yankin Gurin na Karamar Hukumar Fufore a Jihar Adamawa, inda aka gano gawarwaki 11, wasu kuma suka ɓace.
Za a iya tunawa a a watan Yuni a Karamar Hukumar Patigi, Jihar Kwara aka samu hatsarin kwalekwale mafi muni da ya yi ajalin mutum sama da 100 a hanyarsu ta dawowa daga bikin ɗaurin aure a Jihar Neja.
Alkaluman mamata
Alkaluman da Aminiya ta tattaro daga hadduran kwalekwale da suka auku sun nuna mutum 936 suka riga mu gidan gaskiya a dalilin hakan a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata a jihohin Legas, Neja, Kwara, Kebbi, Adamawa, Nasarawa da kuma Akwa Ibom.
2020:
A shekarar 2020, mutum akalla 131 ne suka rasu, wasu da dama kuma suka ɓace a hatsarin kwalekwale a jihohin Anambra, Cross River, Bauchi, Legas, Binuwe Neja, da Sakkwato, da sauransu.
2021:
Mutum 281 kuma sun gamu da ajalinsu, wasu da dama suka bace a irin hakan a jihohin Sakkwato, Bayelsa, Legas, Kano, Neja, Taraba, Ondo, da Kebbi, da dai sauransu.
A shekarar ce mutum 156 suka rasu a hatsarin kwalekwale a tsakanin kauyukan Warrah da Tsihuwan Labata da ke Karamar hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi.
2022:
Kawo yanzu shekarar 2022 ce aka fi samun mace-mace a hatsarin kwalekwale, da mutum 313.
2023:
A shekarar 2023 da muke ciki, zuwa yanzu mutum 216 aka samu alkaluman rasuwarsu a sanadiyyar hakan.
Dole gwamnati da dauki mataki —Kwararru
A kan haka ne masana suka jaddada wajibcin gwamnati a matakin jihohi da tarayya su yi abin da ya kamata na ingantan ɓangaren sufuri da albarkatun ruwa na cikin gida, saɓanin yadda yanzu yake kara-zube, yake ta lakume rayukan al’ummar ƙasa.
Dalilan hatsarin jirgin ruwa
1- Lodin wuce kima: Farfesa a fannin sufuri, Samuel Odewunmi, ya bayyana cewa lodi fiye da misali da ake wa kwalekwale shi ne babban musabbabin hadduran da ke aukuwa.
“Yawancin direbon na daukar kaya fiye da ƙima, saboda haka da zarar igiyar ruwa ta kaɗa, jirgin zai iya kifewa.
2- Lafiyar kwalekwale: “Na biyu shi ne yanayin jiragen ruwan, inda yawanci za ka samu ana tsakiyar tafiya a kan ruwa, sai injin jirign ya mutu, wanda yawanci hakan na faruwa ne idan aka samu cikar ruwa sosai. Da hakan sai kwalekwalen ya fara karkacewa, a ƙarshe dai ya kife.”
3- Shaye-shaye: “Na taɓa zuwa Igbokoda a kwalekwale domin gudanar da wani bincike, abin da na gano shi ne yaran da ke tuƙa su, na yin shaye-shaye kafin su kama hanya da fasinjoji.”
4- Rashin doka: “Inda ake da doka ma, kamar Jihar Legas da ke da hukumar ruwa na cikin gida (LASWA) na ta, ba a tsaurara dokar. Kamata ya yi kafin ƙarfe 7 na dare an rufe sufurin ruwa, amma sai ka samu suna aiki a cikin duhun dare, wannan ai rashin doka ce.”
Hanyoyin magance matsalar
Wani kwararre a fannin sufuri, Dokta Kayode Opeifa, ya bayyana wa wakilinmu wasu matakai biyar da za a bi don takaita yawan mace-mace a kwalekwale a Najeriya kamar haka:
1- Gwamnatin Tarayya da jihohi su tsaya kai da fata wajen aiwatar da matakan tsaro da aminci ga masu mu’amala dabangaren.
2- Jihohi da majalisunsu su kafa hukumominsu na kula da sufurin ruwa na cikin gida.
3- A sanya mafi ƙarancin abin da ake bukata ga duk wanda zai yi harkar sufuri ta kwalekwale.
4- Tantancewa da kuma tabbatar da cikakkiyar lafiyar kowane kwalekwale — bisa dokokin da aka tanadar.
5- Haramta tafiya a lokuta masu hadari, kamar lokacin da iska mai karfi take kaɗawa ko ruwa ya cika fiye da ƙima.
Masanin ya ce, “Sufurin ruwa ba wai kawai a ɗebi mutane a zuba a cikin kowane irin kwalekwale ba ne. Dole sai kwalekwalen da kayan aikinsa sun kasance masu aminci.
“Sannan akwai dokoki da ka’idojin da suka danganci ruwan shi ƙansa – saboda akwai lokacin da ya kamata a shiga a kwalekwale akwai kuma lokacin da bai dace ba, da dai sauran matakan kariya da ya kamata gwamnati ta samar.
“Amma yanzu wannan abin da ake yi, kara zube ne.”
Daga: Sagir Kano Saleh, Haruna Ibrahim (Abuja), Kabiru R. Anwar, Amina Abdullahi (Yola), Abdullateef Aliyu (Legas) & Abubakar Akote (Minna)