✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yaron mota ya fado daga saman tirela tana cikin gudu a Legas

Wani yaron mota da ba gano ko wane ne ba ya rasu bayan da ya fado daga saman babbar motar uban gidansa a yayin da…

Wani yaron mota da ba gano ko wane ne ba ya rasu bayan da ya fado daga saman babbar motar uban gidansa a yayin da take cikin tafiya a Gadar Otedola da ke yankin Berger Bus Stop a Legas.

Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Legas (LASTMA) ta ce yaron motan ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da motar ta dauko buhunan alkama, inda ta wuntsula, duk kayan cikinta suka zube, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata.

Kakakin hukumar, Adebayo Taofiq, ya ce motar ta kwace wa direbanta ne bayan da burkinta ya ki kamawa a lokacin da yake tafiya a guje a cikin ruwan.

“An tsinto gawar yaron motar a karkashin Gadar Otedola, inda jami’an LASTMA suka mika ta ga jami’an hukumar kula da muhalli (SEHMU),” in ji jami’in.

Ya ce hatsarin ya haifar da cunkosun ababen hada a yankin Berger, wanda hakan ya sa masu bi ta 7Up-Berger suka yi ta komawa ta babbar  hanyar Legas-Ibadan.

Amma ya ce “Daga baya an kwashe kayan alkaman a wata mota, aka bude bangaren titin da ya toshe da misalin 5:30 na yamma da hadin gwiwar ’yan sanda, da jami’an hukumomin LASEMA, SEHMU, da sauran jama’a.”