✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gabagadin giringidimin giwaye

Gwaurikikin gwauron gwagware Gwankin giwaye Gwagwagwar agwagin koramar kauye Gabagadin  gwanaye Gantalin gangare Burga da baragadar burgewa barambaramar barewa batagari na bararajewa Birgimar juyin juyawa…

Gwaurikikin gwauron gwagware

Gwankin giwaye

Gwagwagwar agwagin koramar kauye

Gabagadin  gwanaye

Gantalin gangare

Burga da baragadar burgewa

barambaramar barewa

batagari na bararajewa

Birgimar juyin juyawa

balibalin balbalcewa

Zabarin zomaye

Zungurar zungurun zagaye-zagaye

Zamanin zaburar zaki ya zuganye

Zuga-zugin zazzabi ya zagaye

Ziryar ziyarar zirga-zirgar alaye

’Ya’yaye

Da iyaye

’yan tagwaye

dan nagoye-nagoye

Har ma dan yaye

’Ya’yan Inna da Baba

Farfajiyar gidanku mai makuba

Shi ya sa kuke ’ya’yan Abba

Sirara da masu kiba

Wasunu sun zam ’yan daba

Haurobiyawa na jaye-jaye

Balaguro babu waiwaye

Watangaririyar wawaye

Walle-wallen bebaye

Walawalar wautar shaye-shaye

Hikayoyin Hau-hawar hawan sa

Hayaniyar sa-in-sa

Harigidon ’yan wasa

Hargowar harasa

Hatsaniyar cin gurasa

Tatsuniyar gizo da koki

’Yar bora da ’yar mowa

Zaluncin dabobin dawa

kankana na ta kokowa

An shige rukuki

Logar luggar Larabcin Larabawa

Burgar Ingilishin Birtaniyawa

Azarbabin artabun Amurkawa

Sasarin sunkurun Sinawa

Fara’ar farin cikin Faransawa

Jaruman jama’ar Jamusawa

Janjamin juriyar Japanawa

Katantanwar Koriyawa

Rugugin ranwar Rashawa

Tattalin tara taron Turawa

Gangamin gambarar Gambarawa

Kuntukun kidan kukumar Kunkumawa

Gwagwiyar goribar Gabasawa

Yayime-yayimen Yammatawa

Gilu-gilun gittawa

Saurayin-kirinki

Ka ci ganyen bariki

Ka zama mutumin kirki

Kafin a busa maka kakaki

Har ma a maka burki

Akuyar-maman-daudu

Ba ta awo da mudu

Waskiyarta ta kai Wagadugu

Miyagu sun yi gungu

Za su ruga da gudu

An kyallaro su a tudu

Wakilan rafkiya

Al’ummarku ta zam rakiya

Kuna a karafkiya

Haurobiyawa na tankiya

Kun dai iya danniya

Iro Mugun Madambaci

Yana ta fada kamar kyalkeci

Don fitar da a’umma kunci

Myagu nai masa butulci

Sun nuna ba sassauci

Baban-burin-huriyya

Ka da ka karaya

A kada a raya

Sai an gyara Haurobiya

Talaka ya samu abin tutiya

Gabagadin giringidimin giwaye a harkokin tafiyar da kasar nan na kawo  wa Haurobiyawa tarnaki, siyasa ta zama SIYASAR-YASAR SIYASSA, watakila ma shi ya sa ake ta sulalewa da sulalla, illa dai kawai mu ji a salansa;  zamantakewa ta zama ZAMAN-TATTAKEWA, yayin da tattalin da muke kwata TATTALIN TARON TURAWA ya rikide zuwa TURMUTSITSIN TURERENIYAR TUTTULE TULU. A  irin wannan yanayi dole ne mutum ya bijiro da tambayar neman sanin GWAURIRIkIkIN GWAWARE GIWAYEN GIWAYEN da ke yi mana  WAKA-CI-KA-TASHI?

Masu gigiwar aikin gabagadi cikin giringidimin abu abin da suke yi wa al’umma illa BURGAR BAGU DA BARAGADAR INGILISHIN BIRTAIYAWA,  alhali su ne manyan ’yan wawa da ke kawo wa kasar nan tarnaki, tare da jefa jama’a cikin surukuin rukuki.

Haurobiyawa mun fasko jirgin Majalisar Saurayn-kirinki da mataimakinsa Akuyar-maman-daudu, wadanda ke kamfatar dukiya ba tare da wani mudun awo ba. Su ma wakilan rafkiya ba a bar su a baya ba, musamman ma in an yi la’akari da TAbARGAZAR TAKUN SAkAR DOGARI DA kOFATON MAJALISAR. daukacin wadannan al’amura da ake ta tsuwurwurtawa su ke haifar da KASHIN SHA-KUSHE, al’amarin da ke bai wa tika-tika, gunduma-gunduma da suka danne al’umma damar handama da wawura da babakere, domin a akwatin Magana mai jini an taba ruwaito yadda masu karfa-karfa suka yi KUSHEWAR KUdI. Irin wadannan rukunonin al’umma sun salwantar da dukiyar kasa ta yadda ’yan lelensu ma ba za su ci gajiyarta ba.

’Yan makaranta masu koyon watsattsake da buda wagagen littafai a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya ya kamata a fasko cewa, wadanda ke yashe mana dimbin dukiya su yi ta KWASHI-KWARAF, suna yi ne bisa doron abin da kwakwalwarsu a wassafa musu na son kai da son rai a tsarin MAJAUJAWAR MANHAJAR HAJIJIYAR  JAN kARI.

Mai danboto ta shafe shekaru sili da manuniyar sama tana jan RIGIMA, maimakon RAGAMA, har an rasa makama, sai aka samu jam’iyyar TSNTSIYA, amma ita ma ana yunkurin haifar mata da TSIYA-TSIYA. Domin yanzu Babanburin-huriyya ya sanya ai amfani da TUNANIN-BUNU wajen warware tuka da warwarar wadanda suka murtuke fuska suka sha KUNU, watakila ma a kara dama musu wani kunun da ruwan jikakkiyar UNGURNU. Mu dai ba za mu yarda a yi mana sakiyar da ba ruwa ba, ila dai kawai a dumfari masu ciwon KURKUNU.

Lallai akwai bukatar a inganta tsarin koyon watsatake da buda wagagen littatafai, inda za a baje ilimi a faifai don manhajar iliminmu ta shawo kan GABAGAdIN GIRINGIdIMIN GIGIWAR GIWAYE, a rika aiwatar da komai kai WAYE, don kada a mayar da mu WAWAYE. daukar irin wannan matsaya ta zama dole, tunda an rigaya an mayar da cibiyoyin koyon dabarun zaman rayuwa sun zama MAKARANSUWA, ta yadda idan ba ka da abin jinka wa masu fura mai kyau ko sakanni-in-dire da jam’in jami’ar jami’o’in Haurobiya sai dai ’yan dugwi-dugwi su yi ta TSUWWA.

A irin wannan yanayi dai kolo da titibiri an tattake su, tunda GARGAdIN GARADA ya yi GARDAMA, shi kuwa ALARAMMA tuni ya rasa rikar MAKAMA a doron tafiyar zamani.

Haurobiyawa mu hada karfi da karfe wajen hana GABAGAdI GIRINGIdIMIN GIGIWAR GIWAYE, ta hanyar samar da manhaja mara hajijiya, wadda za ta samar da managartan jagorori ba ’YAN JIGARI-JIGARI ba.