Shugabannin Kasashe mafi karfin tattakin arziki a duniya da ake kira G7, sun cimma matsayar samar da rigakafin allurar COVID-19 guda biliyan daya don yaki da cutar a fadin duniya.
Kasar Birtaniya, wadda ita ce mai masaukin baki na taron G7 na wannan shekara, ta sanar da yunkurin kasashen na samar da rigakafin kafin 2023, inda tace za ta samar da na ta tallafin rigakafin allurar a 2022 guda miliyan 100.
Kazalika, ana sa ran Shugabannin kasashen za su tattauna kan lamarin da ya shafi sauyin yanayi.
Wannan shi ne taro na farko da kasashen za su halarta tun bayan wanda aka gudanar a 2019 a kasar Faransa, kafin barkewar annobar COVID-19.
Sannan wannan ita ce ziyara ta farko da sabon zababben Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden ya kai kasar ta Birtaniya tun bayan hawansa mulki.
Taron za a fara shi ne ranar Litinin 14 ga Yunin 2021, wanda tuni masu sharhi kan sha’anin siyasa da sauran al’amuran yau da kullum ke ganin taron zai tattauna muhimman batutuwa da duniya ke ciki.