✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fyade: Kotu ta tsare dan shekara 57 da ya lalata yarinya

Kotu ta umarci a tsare wani dan shekara 57 da ake tuhuma da yin lalata da yarinya ‘yar shekara goma sha biyu. Mutumin ya yi…

Kotu ta umarci a tsare wani dan shekara 57 da ake tuhuma da yin lalata da yarinya ‘yar shekara goma sha biyu.

Mutumin ya yi ta lalata da yarinyar fiye da sau 10 a lokuta daban-daban, inda ya kan kira ta ya ba ta naira 100 a duk sadda zai yi lalata da ita, a cewar ‘yan sanda.

Dan sanda mai gabatar da kara ASP Adegoke Taiwo ya shaida wa Kotun Majestare da ke zamanta a Oshogbo a jihar Osun cewa tsohon ya aikata laifin ne a watan Mayu a yankin Ejigbo a jihar Osun.

Mai gabatar da karar ya ce laifin ya saba Dokar Kare Hakkin Yara Sashi na  31(1)(2), 32 na kundin gwamnatin jihar Osun na shekarar 2007 sashi na 360 na dokar manyan laifuka na jihar da sashe na 34 na shekarar 2002.

Alkalin kotun Uwargida Riskat Olayemi ba ta saurari hakuri da wanda ake tuhuma ya gabatar ba, inda ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi zuwa lokacin da za a mayar da karar kotun Majestare ta Ejigbo.