Mutanen gari sun lakada wa wani wanda ake zargi da bai wa ’yan bindigar Kaduna bayanai har sai da mutu, sannan suka kone gidansa.
Wasu fusatattun matasa ne dai suka yi wa gidan mutumin mai suna Abdullahi Mohammed Gobirawa kawanya, sannan suka kashe shi tare da matarsa da kuma dansu.
- Iyaye sun fara sayar da ’ya’yansu don sayen abinci a Afghanistan
- Najeriya za ta fuskanci tsadar abinci a 2022 — NBS
A cewar Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Tsaro na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, mutanen sun fusata ne sakamakon zargin da ake musu da hannu a ayyukan ’yan bindiga a yankin musamman a ’yan kwanakin nan.
Ya ce bayan kashe mutanen kuma, matasan sun kwashe kayan gidan sannan suka banka masa wuta.
Aruwan ya ce Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi Allah-wadai da yadda mutane suka dauki doka a hannunsu, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci hakan ba a nan gaba.
Daga nan Gwamnan ya umarci jami’an tsaro su gudanar da zuzzurfan bincike a kan lamarin.