✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fusatattun matasa sun kone mutum 3 kurmus bisa zargin garkuwa

Wasu fusatattun matasa sun kone mutum uku kurmus bisa zargin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a garin Akpabuyo dake jihar Ribas. Lamarin dai…

Wasu fusatattun matasa sun kone mutum uku kurmus bisa zargin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a garin Akpabuyo dake jihar Ribas.

Lamarin dai ya faru ne da tsakar ranar Asabar bayan da dubun mutanen ta cika.

A cewar wasu da abin ya faru a kan idonsu, wadanda ake zargin na kokarin sace wani mutum ne lokacin da aka kama su bayan ya kwarmata musu ihu.

Hakan ne ya jawo hankalin makwabtan wajen cafke mutum ukun ta hanyar amfani da makamai daban-daban, ciki har da falankan katakwaye da karafa.

Daga nan ne suka kwace baburan da masu garkuwar suka zo da su, suka sassara musu kai kana daga bisani kuma suka cinna musu wuta.

An dai yi amannar cewa yawancin wadanda ake sacewa a yankin akan tafi da su garin na Akpabuyo ne.

Jim kadan da faruwar lamarin ne dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdulkadir Jimoh ya fitar da sanarwa da bakin kakakinsa, Irene Ugbo yana Allah-wadai da shi.

Ya ja kunnen mutane kan su guji daukar doka a hannusu.

“Da wannan sanarwar, rundunarmu na gargadin jama’a kan su rika amfani da dokokin kasa a kullum a matsayin ma’aunin kowanne irin mataki da za su dauka. Da zarar mun kama masu wannan danyen aikin dole su fuskanci fushin hukuma,” inji kwamishinan.

%d bloggers like this: