Hukumomin kasar Iran sun ce fursunoni takwas ne suka rasu, wasu akalla 50 kuma sun jikkata sakamakon tarzoma da gobara a Gidan Yarin Evin da ke birnin Tehran.
Ma’aikatar Shari’ar kasar ta sanar cewa fursunonin da suka rasu ya karu zuwa takwas ne bayan wasu hudu da aka kai asibiti ranga-ranga bayan gobarar ta ranar Asabar da dare sun ce ga garinku nan.
- An gano bututun satar mai a kusa da sansanin soji
- Sarkin Kano ya ziyarci birnin Marrakesh na Morocco
Da haka ne, “Adadin wadanda suka rasu a gobarar da kuma tarzomar gidan yarin ya karu zuwa takwas,” in ji ma’aikatar ta shafinta na intanet, Mizan.
Tun da farko ma’aikatar sharia’ar ta sanar cewa, “Fursinoni hudu ne suka mutu sakamakon shakar hayakin da gobarar ta haddasa, sannan wasu 61 suka jikkata.”
Sanarwar ta ce wasu hudu na cikin “mawuyacin hali, amma an yi nasarar kashe gobarar.
Tarzomar gidan yari
Rikicin gidan yarin ya kara tayar da hankalin mahukuntan Iran, kari kan zanga-zangar da aka kwashe wata guda ana yi saboda mutuwar Mahsa Amini — wadda ake zargin ’yan Hisbah sun kashe saboda shigar da ta saba wa addini.
Hukumomin kasar sun dora alhakin tashin gobarar a kan “tarzoma da fadace-fadace” a tsakanin fursunonin, amma kungiyoyin kare hakkin dan Adama sun ki yarda da bayanan gwamnatin kasar ba.
’Yan uwa da kungiyoyin kare hakkin fursunonin sun bayyana fargaba, kuma sun ce hukumomi sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a gidan yarin.