✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani sun fara tona asirin masu garkuwa da mutane a Taraba

Kungiyar ta ce za ta cika alkawarin da ta dauka na tona asirin bata-garin cikinsu.

Shugabannin Kungiyar Fulani Makiyaya (Miyetti Allah) sun mika wasu mutane 11 da ake zargi da aikata laifukan garkuwa da mutane ga rundunar ‘yan sanda a Jihar Taraba.

Shugaban kungiyar reshen jihar, Sahabi Tukur ya bayyana cewar sun yi haka ne sakamakon alkawarin da suka daukar wa Sarkin Muri, Abbas Tafida na tona asirin bata-garin cikinsu.

Tukur, ya ce sun kafa wani kwamiti a tsakaninsu da ya kunshi bangarorin Fulanin da ke jihar da za su yi aiki da jami’an ‘yan sanda a kananan hukumomi 16 domin zakulo masu garkuwa da mutane a cikinsu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abimbola Sokoya ya yaba da matakin da kungiyar ta dauka na taimaka wa harkar tsaro a jihar.

Sokoya, ya kuma bukaci samun hadin kai tsakanin jihohin Adamawa da Benuwe da kuma Taraba domin dakile ayyukan garkuwa da mutane da wasu laifuffukan da suka addabi jama’a, yayin da ya sha alwashin bai wa Fulanin goyon bayan samun nasara.

Wasu masu garkuwa da mutane guda shida da suka tuba a wurin, an basu Alkur’ani mai girma sun rantse cewar ba za su sake aikata laifin ba ko kuma satar shannun jama’a.

A watannin da suka gabata Sarkin Muri Abbas Tafida, ya sha alwashin daukar mataki mai tsauri na kashe ‘yan uwan mutanen da suka addabe su wajen garkuwa da mutane ko satar shannu ko kuma kashe jama’a a yankin.