Shugabannin kungiyar Miyatti Allah sun karyata zargin da aka yi masu, cewa suna shirin kai hari garin Mambilla na Jihar Taraba da nufin ramuwar gayyar ta’annatin da aka yi masu watanni hudu da suka gabata.
Shugaban Miyatti Allah a Jihar Taraba, Sahabi Mahmud Tukur ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Jihar Adamawa, a lokacin da suka gudanar da wani taro na musamman na membobinsu da ke Arewa maso gabas dangane da irin abubuwan da ke faruwa da su.
Sahabi ya karyata wannan zargi da ake masu sannan ya bayyana cewa, wannan batu kazafi ne da wasu manya kuma masu hali a kasar ke shirin dauka a kansu. Ya ce wadansu ne da ba ’yan kasa ba su sake kai hari Mambilla da sunan ’ya’yan kungiyar ta Miyatti Allah.
Ya kara da cewa ziyarar da Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishiyaku ya kai wa Shugaba Buhari, inda ya bukaci a karo wa Jihar Taraba sojoji ba gaskiya daidai ba ne, illa wata hanya ce ta yaudara da kuma sanya tsoro a cikin jama’ar Taraba.
Tukur ya sake jaddadawa cewa: “Muna son mu fada wa jama’ar Jihar Taraba da duka ’yan Najeriya cewa, Fulani makiyaya ba su taba kisa ba kuma ba za su yi kisa ba a kan kowa, sun gwammace su kai kara kotu kuma kotu ta shiga tsakaninsu da masu kazafi.”
Shugaban Miyatti Allah na Arewa maso gabas, Mafindi Umaru danburam ya ce bisa ga bincike da suka gudanar, Fulanin Jihar Taraba da na Najeriya ba su da damuwa da mutanen Jihar Taraba da kuma na kasa ba ki daya, balle su ce za su kai masu hari. “Abin bai yi dadi ba, tun da masu kisa a Mambila dauko su aka yi haya daga wasu kasashen waje. Muna kira ga Shugaba Buhari da ya sake gudanar da bincike game da ainihin masu tafka wadannan laifuka,” inji shi.
Dangane da dokar da ta shafi makiyaya a jihar ta Taraba da ake tsammanin fara aiki da ita a 2018, danburam ya ce wannan shirin doka da Majalisar Dokokin jihar ta sanya wa hannu, ya ce Gwamna Ishaku Darius ko sau daya bai taba zuwa wajensu ba. Amma ya ce ba su yi mamakin hakan ba, tun da ya zargi gwamnan da cewa tun farko sun fahimci yana korar su ne daga jahar.