✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani makiyaya na ficewa daga Taraba saboda yawan kai musu hari

Makiyayan sun ce za su koma inda suka fito saboda ana kashe su

Dubban mata da ’ya’yan Fulani makiyaya na tserewa daga sassan yankin Baruwa da ke Karamar Hukumar Gashaka ta Jihar Taraba, zuwa wasu sassan kasan nan.

Aminiya ta iske mata da ’ya’yan Fulani a babbar tashar motar Jalingo a kan hanyarsu ta zuwa Abuja da wasu sassan Jihohin Neja da Kwara da Gombe.

Wasu daga cikin wadanda wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa sun tsare daga inda suke zaune da dabbobinsu saboda hare-hare da wasu masu dauke da bindigogi ke kai wa rugagensu, inda suka yi zargin an halaka makiyaya masu yawan gaske.

Wani makiyayi mai suna Abdullahi Ja’e, ya ce ana kai musu hari ana halaka su sannan kuma an an umarci dukkan wani bakon makiyayi da ya shiga Jihar Taraba ya fice.

Ya ce makiyayan sun je Taraba ne daga jihohin Neja da Kwara da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, domin a can ma ana halaka su ana kwace musu dabbobi.

Abdullahi ya kara da cewa ba su da wani zabi face su bar jihar zuwa inda suka fito.

Amma wakilin Aminiya ya fahimci cewa mata da ’ya’yan makiyaya ne kawai suke ficewa daga jihar, amma ba mazaje ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatare wa wakilin namu cewa rundunar ba ta da labarin kai wani hari a mazaunin makiyaya a garin na Baruwa, kuma ba ta sami wani korafi kan korar makiyaya daga yankin ba.