Shugaban Cocin Methodist Church of Nigeria, Akbishop Samuel Uche, ya yi zargin cewa Fulani da Kanuri (Barebare) da ke neman mulki ido rufe ne suke tallafa wa hare-haren Boko Haram.
Akbishop Samuel Uche ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wajen addu’o’in tunawa da mazan jiya da aka gudanar a Cibiyar Kiristoci ta kasa da ke Abuja.
Shugaban cocin ya bayyana haka ne a gaban Shugaba Goodluck Jonathan da Shugaban Majalisar Dattawa Dabid Mark da manyan shugabannin sojoji da sauran manyan mutane, amma ba wanda ya ce komai a kan hakan.
Ya ce, sojojin da suke fagen fama sun shaida masa shi da sauran bishop-bishop cewa baya ga abokan hadin gwiwa daga kasashen Chad da Libya da Somaliya, kashi 95 cikin 100 na wadanda suke yaki da Najeriya Fulani ne da Kanuri.
Akbishop Uche ya ce, ba domin sanya hannun wasu makiya kasa ba, da tuni an magance matsalar hare-haren Boko Haram.
Ya ce, wadannan makiya kasa suna amfani da matsalar wajen cimma burinsu na siyasa tare da zargin gwamnati mai ci kan gaza yin komai don magance ta’addanci.
Shugaban ya ce, wadanda suke zagon kasa ga yaki da ta’addanci da wadanda suka bari ana amfani da su “suna cikin manyan ’yan siyasa, wasu suna cikin sojoji da sauran hukumomi.”
Ya kara da cewa, wadanda suka tallafa wa hare-haren suna son Musuluntar da Najeriya ne tare da kafa wata daular a bayan Daular Sakkwato, inda ya ce hakan ba zai taba yiwuwa ba.
Ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri daga kowane bangaren jama’a na “Kiristantar ko Musuluntar da Najeriya aikin baban giwa ne da ba zai samu nasara ba, saboda hakan ba zai faru ba, sai dai in muna son jefa kanmu a cikin bala’i ne.”
Akbishop Uche ya “Wadannan miyagun ’yan kasa maza da mata da suka mayar da kansu makiya Najeriya. Wadannan mutane suna zagon kasa ga duk wani yunkuri na kawo zaman lafiya da gwamnati ke yi a Arewa maso Gabas. Wasu daidakun mutane marasa kunya da kungiyoyi na suna fadin wasu furta wasu kalmomi tare da amfani da mummunan halin da ake ciki a matsayin makamin neman goyon bayan siyasa suna zargin gwamnati da gaza yin komai don magance matsalar hare-haren. Wane ne yake yaudarar wani? Na yi imani ’yan Najeriya suna da wayo kuma mutanennmu sun san cewa zagon kasa ne ke kawo tarnaki ga sojojinmu su kwato ’yan matan Chibok.”
Ya kara da cewa, “Bari in fallasa muku a wannan yammaci a wannan addu’a mai muhimmanci a daidai wannan lokaci cewa wasu sojojinmu, saboda kun san mu bishop-bishop muna da matsayi a cikin al’umma, muna hulda da sojoji da sauran nau’o’in mutane. Wasu daga cikin mutanen da suke fagen daga sun shaida mana cewa baya ga sojojin haya daga Chadi da Libya da kuma Somaliya, kashi 95 cikin 100 na wadanda suke yakar kasarmu Fulani ne da Kanuri. Sun fusata ne saboda suna bukatar mulki ta kowace hanya. Sun dauka Najeriya tasu ce su kadai, kuma an haife su ne don su yi ta mulki saura kuma oho. Wannan yaudara ce kawai.”
Akbishop Uche ya ci gaba da cewa: (Na biyu suna son Musuluntar da Najeriya ne, su kafa daular Musulunci daban da wadda muka sani a Sakkwato.”
Akbishop ya ce masu barazanar kafa gwamnatinsu ta daban bayan zaben da ke tafe sun co amanara kasa, don haka, “Don haka kamata ya yi a ce suna kurkuku saboda sun ci amanar kasa.”
Ya bukaci sojoji cewa’, “Duk wani dan takarar Shugaban kasa da ya yi ba daidai ba, kamata ya yi a daure shi na akalla shekara 12.”
Ya ce za a murkushe Boko Haram, inda ya bukaci gwamnati ta samar wa sojoji makamai da kula da su da kuma kula da mata da ’ya’yan sojojin da suka mutu a fagen daga.
Tunda farko Shugaba Jonathan ya nanata zarginsa na cewa akwai masu zangon kasa a cikin sojojin Najeriya. “Ina yaba wa sojoji, duk inda kuka ji an kashe mutane akan samu zargin cewa ba su yin komai. Eh, akwai masu zagon kasa a cikin sojojin, babu shakka a kan haka, an kama wasu, wasu ma an yanke musu hukunci.”
Ya kara da cewa “A gwamnatance mun san cewa akwai rashin wadatattun sojoji, amma ina tabbatar muku muna kokari a wannan lokaci domin wajen samar da kayan aiki domin kare ’yan kasarmu.”