✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fulani da Irigwe sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Al’ummomin kabilun Fulani da Irigwe da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, sun sanya hannu kan jarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.

Al’ummomin Fulani da Irigwe da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, sun sanya hannu kan jarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.

Shugabannin kabilun biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar ce a gaban Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, a gidan gwamnatin jihar da ke garin Jos.

Shi dai yankin Bassa, an yi shekaru da dama ana fama da rikice-rikice, tsakanin al’ummomin Fulani da Irigwe.

Da yake jawabi a taron sanya hannu kan yarjejeniyar, Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ya bayyana farin cikinsa da matakin da al’ummomin suka dauka.

Ya bayyana cewa a taron, shugabannin al’ummomin sun nuna wa duniya cewa sun gaji da rikice-rikice a yankinsu, don haka suka kudiri aniyar yafe wa juna, don kare faruwar rikici-rikice a nan gaba.

Ya yaba wa shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki na yankin, kan wannan mataki na zaman lafiya da aka dauka.

A nasa jawabin, Sarkin Miango, Rebaran Ronku Aka, ya gode wa Gwamna Lalong, kan kokarinsa na ganin an sami zaman lafiya a wannan yanki da jihar baki daya.

Ya ce al’ummar Bassa suna son su manta da abubuwan bakin cikin da suka faru a baya, don ganin sun sake dawo da zaman lafiyar da aka san su da shi a da.

A wajen taron, shugabannin kwamitin tsaro da zaman lafiya na Karamar Hukumar Bassa, John Power da Alhaji Ya’u Idris ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar a madadin wadannan al’ummomi.