✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani da Berom sun yi bikin zaman lafiya a Filato

Al’ummar Fulani da na Berom mazauna Gundumar Gashish da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi a Jihar Filato sun gudanar da gagarumin biki don nuna farin…

Al’ummar Fulani da na Berom mazauna Gundumar Gashish da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi a Jihar Filato sun gudanar da gagarumin biki don nuna farin ciki da wanzuwar zaman lafiya bayan gundumar ta yi fama da munanan hare-hare a baya.

A yayin bikin an ci, an sha, an kuma gudanar da raye-raye da kade-kade masu ban sha’awa da kuma nishadantarwa.

Rundunar Samar da Tsaro a Jihar Filato (OPSH) ta shirya bikin da aka gudanar a Makarantar Sakandaren Pilot Science da ke Kakuruku a Gundumar Gashish.

Bikin wanda ya gudana a ranar Asabar din makon jiya ya samu halartar jami’an tsaro da shugabannin Fulani da na Berom da ’yan siyasa da yara da matasa.

A yayin bikin Rundunar OPSH ta yaba wa Liman Abdullahi Abubakar wanda a bara ya tseratar da Kiristoci 300 daga wadansu mahara da suka kawo hari kauyen Ngar Yelwa da ke karamar hukumar.

A jawabin Kwamandan Rundunar (OPSH), Manjo Janar Augustine Agundu ya ce rundunar za ta ci gaba da cizawa da busawa har a samu zaman lafiya mai dorewa ba ma a yankin Gashish kawai ba har a fadin Jihar Filato.

Ya ce, “Ba za mu zuba ido wadansu ’yan kalilan da ba su wuce 10 zuwa 20 su rika tayar mana da zaune-tsaye ba, don haka rundunata za ta rika cizawa da hurawa har zaman lafiya ya samu tsaya da kafafunsa ba a Gashish kawai ba har da fadin Jihar Filato.” Janar Agundu ya ce rundunarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da duk wanda ya ki yarda a zauna lafiya.

Idan ba a manta ba kauyukan Gundumar Gashish sun yi fama da hare-hare a shekarun baya, inda ko a ranar 24 ga Yunin bara an ce akalla mutum 200 aka kashe  a wani hari da aka kai kauyuka 11 da ke gundumar.

Bayan hari ne Rundunar OPSH ta kara jami’an tsaro a gundumar, sannan ta shirya tattaunawa a tsakanin Fulani da Berom, inda tattaunawar ta haifar da zaman lafiya a gundumar.

A lokacin da yake jawabi, Ardon Gashish, Idris Gidado ya bukaci Fulani da Berom su zauna lafiya, sannan su guji tashin hankali. Ya ce, “An halicci dan Adam daga Annabi Adamu da kuma Hauwa’u ne, sannan Allah Ya sa mutane a kasa-kasa, wasu a Afirka, wasu Asiya da Turai, sannan ya sa mutane su kasance kabilu daban-daban, wasu  Fulani, wasu Hausawa ko Yarabawa ko Berom ko Ibo. Allah Ya halicce mu don mu yi zumunci, mu so juna. Kuma Ya ce mafi kusanci da Shi, shi ne wanda yake tsare dokar Allah, ba ya kashe wani ko aikata miyagun laifuffuka. Don haka ya zama dole mu zauna lafiya da juna.”

A jawabin Dagacin Gashish, Da John Dalyop ya roki gwamnati ta gina gidajen da aka rushe lokacin hare-haren da aka kai gundumarsa.

Dagacin wanda dan majalisarsa Mark Wide ya wakilta ya bukaci Fulani da Berom su yafe wa juna, su dawo da zumuncin da suke yi shekaru aru-aru da suke zaune tare.

Shugaban Kungiyar Matasan Fulanin Gundumar ya bukaci matasan Berom da na Fulani su manta da abin da ya faru a baya, su mayar da hankali kan yadda zaman lafiya zai inganta a gundumar.

Shi ma Shugaban Kungiyar Matasan Magina na Berom, Paul Philips ya bukaci a zauna lafiya, domin sai da zaman lafiya za a samu ci gaba mai dorewa da  bunkasar tattalin arziki.