✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani a Oyo na cikin fargaba sakamakon kashe makiyaya 12

Al’ummar Fulani makiyaya mazauna Iseyin a Jihar Oyo sun shiga fargaba tun bayan da a kwanakin baya suka wayi gari da wani abin alhini bayan…

Al’ummar Fulani makiyaya mazauna Iseyin a Jihar Oyo sun shiga fargaba tun bayan da a kwanakin baya suka wayi gari da wani abin alhini bayan da wasu mutane da suke zargin ’yan asalin yankin ne suka kai masu farmaki a daura da wata korama da suke kiwo, inda suka halaka Fulani makiyaya 12 tare da tarwatsa dabbobin da suke kiwo a wajen.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya a Jihar Oyo, wanda kuma shi ne Sarkin Fulanin lardin Oke-Ogun, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a kwanakin baya, lokacin da al’ummar Yarabawan yankin suka iske wata gawar dan uwansu a daji. “Gawa ce suka gani babu alamun sara ko harbin bindiga ko wani tabo a jikinta, sun sanar da ’yan sanda suka dauke gawar, bayan tafiyar ’yan sandan sai suka yo gayya suka je can inda Fulani ke kiwo a bakin korama; suka far masu, inda suka halaka mutum 12,  kuma mutum 18 sun bace. Abin takaici ne, domin wajen da suka gano gawar babu wani Bafulatani da ke kiwo, ba hanyar shanu ba ce amma kawai suka far mana. Mun yi iya kokarinmu, mun kwantar wa jama’armu hankalinsu, mun hana kowa daukar doka a hannunsu. Tsoron da muke ciki shi ne, babu tabbacin tsaron rayukanmu a wannan yanki,” inji shi.

Shuwagabannin Fulanin yankin sun nuna fargabarsu ta ci gaba da kasancewa cikin rashin tsaro, domin ba su gamsu da yadda jami’an ’yan sanda ke rikon lamarin ba. Sai dai bayan faruwar lamarin Gwamnatin Jihar Oyo ta kira shuwagabannin Fulani makiyaya taron zaman lafiya, taron da ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar, Sanata Abiyola Ajmobi tare da karin wasu wakilan gwamnatin da shuwagabannin al’umma, inda aka tattauna hanyoyin da za a bi don samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, shuwagabannin Fulanin sun yi korafin cewa babu wanda aka kama a kan kisan.