Hukumar Kare Hatsura ta Kasa FRSC a Jihar Gombe suna shirin kaddamar da kamfen din hana gudu da ababen hawa a watannin nan na karshen shekara da ake kira ember months.
Yanzu haka yana shirin gudana ne a tashar mota ta garin Kaltungo da ke Jihar Gombe.
Hukumar ta shirya taron ne da hadin gwiwar shugabanin tashoshin mota na RTEAN da NURTW don fadakar da direbobin illar gudu da daukar kaya fiye da kima a wannan lokaci da ake fuskantar bukukuwan karshen shekara.
Taron yanzu haka ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga kowanne bangare da sauran jami’ai irin su VIO da Civil defence da Mai Kaltungo da Dagatai da Hakimai daga yankin karamar Hukumar Kaltungo
Amma tuni shugaban hukumar ta kare hatsura ta kasa reshen Gombe Abdullahi Sarki Ibrahim tare da jami’an sa sun riga sun zauna ana jiran isowar gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ne kawai.