Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta kaddamar da na’ura ta musamman wadda za ta rika amfani da ita wajen gano direbobi ’yan kasuwa masu ta’ammali da barasa.
Sabuwar na’urar in ji hukumar, za ta yi amfani wajen gwada numfashin direbobi domin gano adadin barasar da suka dirka.
- Zanga-zangar dalibai kan biyan albashin malamansu ta rikide zuwa tarzoma a Taraba
- Hajji 2023: An ba wa jihohi kujerun maniyyata 75,000
Da yake karin haske game da na’urar a ranar Litinin, Kwamandan FRSC na Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce duk direban da aka kama ya kwankwadi barasa wuce kima za a kwace motarsa.
Ya kara da cewa, ba barasa kadai ba hatta sauran abubuwan shaye-shaye masu illa ga jikin dan adam na’urar za ta taimaka waje ganowa.
“Idan a tasha muka gano direba, nan take za mu sanar da jami’ansu kan direban ya sha barasa wuce kima don haka a kwace motarsa.
“Na’urar za ta iya gano komai a jikin mutum, shi ya sa mukan bukaci direbobin su ja numfashi su sake a kan na’urar, ta haka za mu gano idan akwai matsala,” in ji shi.
Ya ce jami’ansu za su rika yawo da wannan na’urar a kan tituna da tashoshin mota domin cika aiki.
Shugaban tashar Bauchi-Kano reshen Awala, Auwal Ibrahim, ya yaba wa FRSC da samar da wannan sabuwar fasahar.