Sabon kocin kungiyar Wolves, Bruno Lage, ya dauko dan wasan gefe na Barcelona, Francisco Trincao.
A yanzu shi ne dan wasan na biyu da Lage ya kawo tun bayan zuwansa kungiyar da ke buga gasar Firimiyar Ingila.
- An kama ‘barawo’ yana bikin zagayowar ranar haihuwarsa
- Shekaruna sun wuce na tsayawa takarar Shugaban Kasa — El-Rufa’i
Dan wasan mai shekara 21 na kasar Portugal ya koma Wolves a wata yarjejeniyar aro da aka kulla da za ta kare bayan shekara daya kacal.
A halin yanzu dai Wolves tana da zabin mayar da kwantaragin dan wasan ya zama na dindindin idan ta biya kimanin fam miliyan 26 kamar yadda kafofin yada labarai na Turai da dama suka ruwaito.
Kungiyar ta dauko Trincao bayan sayen dan wasan baya na kasar Colombia mai shekara 21, Yerson Mosquera.
“Ina kyautata zaton magoya bayanmu za su nishadantu wajen ganinsa ya murza leda a kungiyar, saboda dan wasa ne mai hazaka sosai,” a cewar Scott Sellar, mai bayar da shawara kan wasanni da kuma yadda za a samu nasara a kungiyar.
“Mun dauki tsawon lokaci muna lura tare da zawarcinsa tun yana Braga kafin zuwansa Barcelona saboda dan wasa ne da za a ci moriyarsa bisa la’akari da karancin shekarunsa.
“Duk da cewa shekarunsa basu wuce 21 ba, amma ya buga wasanni da dama a gasar La Liga saboda haka Firimiyar Ingila ba za ta zame masa wani kalubale ba.
A watanni baya dai rahotanni sun bayyana cewa, Barcelona ta sa ran yin musayen dan wasan nata wajen yarjejeniyar dawo da tsohon dan wasanta, Adama Traore zuwa Camp Nou.
A kakar wasansa ta farko a Barcelona, Trincao bai wani taka rawar gani ba yadda aka yi zata.
Hakan ya sanya Barcelona ta yi kokarin mika shi aro zuwa wata kungiyar kuma Wolves na daya daga cikin wadanda suka nuna sha’awarsu kan dan wasan a matsayin aro.
Trincao ya fara murza leda a kungiyar Barga da ke kasarsa ta Portugal, inda ya buga gasar Europa gabanin komawarsa Barcelona a watan Agustan bara.
A kakar wasa ta bara ce dan wasa ya haska a manyan wasanni 42, ciki har da biyar a gasar cin Kofin Zakarun Turai, sannan ya buga wa kasarsa wasanni biyar.