✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fizgen jaka: Kotu ta ba da belin matashi N500,000

Wani matashi mai yin fizgen jakunkuna ya shiga hannu inda aka gurfanar da shi a gaban kotu a Abuja. Jami’an ’yan sanda sun gurfanar da…

Wani matashi mai yin fizgen jakunkuna ya shiga hannu inda aka gurfanar da shi a gaban kotu a Abuja.

Jami’an ’yan sanda sun gurfanar da matashin mai shekara 32 ne bisa zargin aikata kwace, bayan an cafke shi a yankin Nyanya

Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa Kotun Yankin cewa an cafko matashin ne bayan wata wadda ya yi wa kwacen jaka, Hassana Bobboi ta kai koke a caji ofis da ke unguwar Utako.

Ya ce a yayin bincike ’yan sanda sun gano karin wata jakar hannu mallakar wata mai suna Zainab Hassan wadda a cikin jakar aka samu kudi N12,000 da kuma katin shaidarta da katin cirar kudi.

Ya ce hakan laifi ne karkashin Sashe na 292 na dokar ‘Penal Code’; sai dai kuma wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa da aikatawa.

Mai shari’a Yahaya Sheshi, ya ba da belin matashin a kan Naira dubu dari biyar da kuma sharadin wanda zai tsaya masa ya kuma kawo kudin.

Daga nan kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Maris, 2021.