✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fiye da Naira biliyan 400 sun zirare a Gwamnatin El-Rufai — Majalisar Kaduna

Kawo yanzu dai El-Rufai bai yi martani kan wannan zargi ba.

Majalisar Dokokin Kaduna ta yi zargin cewa fiye da Naira biliyan 400 ne suka zirare a mulkin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Majalisar na wannan zargi yayin da ta buƙaci hukumomin da ke yaƙi da rashawa su binciki tsohon gwamnan da wasu muƙarraban gwamnatinsa kan zargin cin amanar aiki da halasta kuɗin haram.

Wannan na zuwa ne bayan bincike na musamman da wani kwamitin majalisar ya gudanar ƙarƙashin jagorancin Henry Magaji Danjuma.

A cewar rahoton da Henry ya gabatar a ranar Laraba, yawancin bashin kuɗin da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin El-Rufai, ba a yi amfani da su yadda suka dace ba, kuma a wasu lokuta, ba a bi ka’idojin da suka dace wajen samun bashin ba.

Rahoton binciken da aka gabatar a gaban majalisar ya zargi El-Rufai da wasu manyan muƙarraban gwamnatinsa da cin amanar aiki da halasta kuɗin haram da cin bashi ba bisa ƙa’ida ba.

Dangane da hakan kwamitin ya bai wa Gwamna Uba Sani shawara da ya nemi hukumomin yaƙi da rashawa su gudanar da bincike da gurfanar da tsohon gwamnan da wasu jami’an gwamnatin kan zargin amfani da muƙami domin bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba, da karkatar da kudaden jama’a, da kuma kuɗaɗe.

Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar, Yusuf Liman ya ce naira biliyan 423 ne suka zirare a lokacin gwamnatin El-Rufa’i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi.

Kawo yanzu dai tsohon gwamnan bai yi martani kan wannan zargi da majalisar take yi a kansa ba.