✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitattun ’yan kwallo 10 da suka gaji iyayensu

Akwai kananan yara da ke son cin gajiyar iyayensu a wani tafarki na rayuwa.

A duk duniya bisa al’ada, akwai miliyoyin kananan yara da suke son bin sahun iyayensu da nufin cin gajiyar iyayen a wani tafarki na rayuwa da suka taso suka ga iyayen a kai.

Irin wannan al’ada ba ta bambanta ba a fagen kwallon kafa, inda akwai zakakuran ’ya’yan wasu fitattun ’yan kwallon da suke son bin tafarki iyayensu.

Wadansu daga cikin ’ya’yan irinsu Kasper Schmeichel, golan Kungiyar Leicester City ko kuma Daley Blind, dan wasan baya da tsakiya na Kungiyar Ajax, sun ci gaba da taka rawar gani wajen taimaka wa kungiyoyinsu zama zakarun gwajin dafi.

A shekarar 2016 ce Kasper Schmeichel ya taimaka wa Leicester City ta lashe gasar Firimiyar Ingila karon farko bayan kafuwarta fiye da shekara 100.

Mahaifinsa, Peter Schmeichel shi ne Golan Kungiyar Manchester United a lokacin samartakarsa.

A duk ilahirin Turai, akwai rukunin sababbin ’yan wasa da ke son gadar mahaifansu da suka yi fice a harkar kwallo, inda suke ci gaba da fuskantar matsin lamba da fafutikar ganin sun maye gurbin nasarar da iyayensu suka samu.

 A yayin da akwai wadanda suka dara wadansu kwazo, sai dai akwai babban aiki a gaban dukkansu da sai sun sha tafiya mai dogon zango a fagen da suka sa a gaba.

Ga jerin ’yan kwallo 10 da ke murza leda a Turai kuma suke son su gaji mahaifansu.

Justin Kluivert

Justin Kluivert

Shekarunsa: 22  Kungiyarsa: RB Leipzig Mahaifinsa: Patrick Kluivert

Justin Kluivert wanda ya fito daga makarantar horon kwallon kafa ta Ajax, yana fatar tauraruwarsa ta haska kamar ta mahaifinsa, Patrick Kluivert.

A shekarar 2017 ce ya haska a wasan karon farko da ya buga wa kungiyar, inda bayan buga mata wasa 56 ya zura kwallo 13.

Dan wasan mai shekara 22 ya samu gurbi a ayarin kasar Netherlands a shekarar 2018, inda ya haska a wasan da kasar ta buga da Portugal.

Babansa ya samu nasarori da dama a Spain da Netherland, ciki har da gasar cin Kofin Zakarun Turai da ya lashe tare da Ajax a 1995.

Marcus Thuram

Marcus Thuram

Shekarunsa: 23 Kungiyarsa: Borrusia Mönchengladbach Mahaifinsa: LilianThuram

Marcus dan Lilian Thuram, a yanzu haka yana taka leda ne a Borrusia Mönchengladbach a matsayin dan wasan gaba, bayan ya sha fama da fuskantar rashin nasara a gasar Ligue 1 ta Faransa, sakamakon fadawa rukunin masu buga Championship a lokacin da yake Guingnamp duk da zura kwallaye 9 da ya yi cikin wasa 32 da ya buga.

Dan wasan mai shekara 23, ya ji dadin kakarsa ta farko a Jamus, inda ya jefa kwallo 10 a gasar Bundesliga, wanda hakan ya taimaka wa kungiyarsa ta kare gasar a mataki na hudu kuma ta samu gurbin shiga gasar cin Kofin Zakarun Turai ta shekarar da za ta gabata.

Isaac Drogba

Isaac Drogba

Shekarunsa: 20 Kungiyarsa: Guingnamp Mahaifinsa: Didier Drogba

Wani zakakurin dan wasa da ya dauki hankalin masoya kwallon kafa saboda shaharar da mahaifinsa Didier Drogba ya yi, shi ne Isaac Drogba na Kungiyar Guingnamp, wanda ya je kungiyar a shekarar 2018 bayan barin makarantar koyar da kwallo ta Chelsea.

Komawarsa makarantar koyon kwallon da ke buga gasar Ligue 2 a Faransa, ta nuna cewa Isaac yana bin sahun mahaifinsa Didier Drogba wanda ya buga wa Gunignamp wasa 50 kafin komawarsa Marseille, inda daga nan ne ya koma Chelsea.

Enzo Fernandez

Enzo Fernandez Zidane

Shekarunsa: 26 Kungiyarsa: Almeria Mahifinsa: Zinedine Zidane

Daya daga cikin ’ya’yan Zinedine Zidane hudu, wadanda dukkansu suka biyo mahaifinsu, shi ne Enzo Fernandez, wanda a yanzu haka yake ci gaba da fafutikar nema wa kansa suna bayan barin Real Madrid, inda a nan ne ya fara taka leda.

A watan Janairun 2018 ne Kungiyar FC Lausanne-Sport ta kulla yarjejeniya da Enzo bayan barin Alaves, inda ya shafe ragowar kakar wasanni a matsayin dan wasan aro A CF Rayo Majadahonda.

Fernandez ya koma Alves ta kasar Portugal, inda ya ci mata kwallo biyu a wasa 10 da ya haska a Primeira Liga gabanin komawa Almeria a matsayin dan wasan aro.

Sauran ’ya’yan Zidane uku da ke suke murza leda su ne – Luca, Theo da Elyaz, wadanda dukkansu suka fara kwallo a matsayin mallakin Real Madrid, sai da a halin yanzu Luca wanda mai tsaron gida ne ya koma Rayo Vallecano.

Timothy Weah

Timothy Weah

Shekarunsa: 21 Kungiyarsa: Lille Mahaifinsa: George Weah

Bayan tashinsa a Amurka, Timothy Weah ya koma Faransa a shekarar 2014, inda ya rika buga wa Kungiyar PSG a cikin rukunin ’yan wasanta masu tasowa kafin kulla kwantaragin shekaru uku da ita inda ya hakan ya maida shi cikin sahun manyan ’yan wasan kungiyar.

A watan Maris na shekarar 2018 ne Timothy ya haska a wasan farko da ya buga wa kungiyar, inda aka sako shi a matsayin canji daga benci a wasan da kungiyar ta doke Troyes da ci 2-0.

Federico Chiesa

Federico Chiesa

Shekarunsa: 23 Kungiyarsa: Juventus Mahaifinsa: Enrico Chiesa

Federico Chiesa, Dan wasan gaba na Juventus, a halin yanzu yana kan tafarkin cin gajiyar mahaifinsa, Enrico Chiesa duk da ya bar Kungiyar Fiorentina.

A shekarar 2016 ce tauraruwar dan wasan ta fara haskawa bayan faranta wa Fiorentina, inda aka zakulo shi daga cikin rukunin ’yan wasan da ke samun horo na koyon Kwallon Kafa.

Erling Braut Haaland

Erling Braut Haaland

Shekarunsa: 20 Kungiyarsa: Borrusia Dortmund Mahaifinsa: Alf-Inge Halaand

Erling Halaand ya fara kwallo ne a mahaifarsa ta Norway a gasar Bryne and Molde, amma daga bisani a shekarar 2019 ya koma RB Salzburg wanda tun daga wannan lokaci tauraruwarsa ta fara haskawa.

Dan wasan ya jefa kwallo 29 cikin wasa 27 da ya buga wa Salzburg, ciki har da takwas da ya ci mata a gasar cin Kofin Zakarun Turai, lamarin da ya sanya Kungiyar Borrusia Dortmund ta fara zawarcinsa.

Daniel Maldini

Daniel Maldini

Shekarunsa: 19 Kungiyarsa: AC Milan Mahaifinsa: Paolo Maldini

A yayin da daularsu ke ci gaba da kafuwa a Kungiyar AC Milan, Daniel Maldini, ya haska a karon farko yayin haduwar Kungiyar da Hellas Verona, inda ya biyo bayan mahaifinsa Paolo Maldini da kakansa, Cesare a matsayin mutum uku ’yan tsatso daya da suka murza leda a Rossoneri.

Sai dai sabanin yadda mahaifinsa ya kasance a matsayin dan wasan baya mafi kyau a tarihin kwallon kafa inda ya lashe gasar SerieA bakwai da ta cin Kofin Zakarun Turai biyar cikin sama da wasa dubu da ya buga wa kungiya da kasa, Daniel yana murza leda a matsayin dan wasan tsakiya ne.

Jonathan Klinsmann

Jonathan Klinsmann

Shekarunsa: 24 Kungiyarsa: LA Galaxy Mahaifinsa: Jurgen Klinsmann

Jonathan Klinsmann ya shafe farkon rayuwarsa ta kwallon kafa a Amurka, inda mahaifinsa, Jurgen yake horar da ’yan wasan kasar.

Bayan ya murza leda a kungiyoyin kwallon kafa da dama a Amurka da kuma tafiyar gwada bajintarsa a Turai, Jonathan wanda mai tsaron raga ne ya samu nasarar kulla yarjejeniya da Kungiyar Hertha Berlin, inda ya shafe shekara biyu duk da cewa, bai taba haskawa ba a matsayin babban dan wasa a kungiyar.

A wasanni da aka yi a 2019 ne Klinsmann ya bar Jamus zuwa Kungiyar St. Gallen da ke Switzerland, amma wasa biyu kacal ya samu damar bugawa.

Tyrese Campbell

Tyrese Campbell

Shekarunsa: 21 Kungiyarsa: Stoke City Mahaifinsa: Kevin Campbell

A watan Fabrairun 2018 ne Tyrese Campbell ya haska a wasan farko a Kungiyar Stoke City, inda yake fatar cin gajiyar mahaifinsa Kevin, amma kafin nan sai ya taimaka wa kungiyar ta hauro daga rukunin masu buga dagaji (Championship) bayan fadawarta saboda rashin nasara a gasar Firimiyar Ingila.

Cikin wasa 325 da ya buga a Firimiyar Ingila a Arsenal da Nottingham Forest da Everton da West Bromwich Albion, Kevin Campbell ya jefa kwallo 82, sai dai duk da wannan bajinta da ya yi, bai samu nasarar lashe gasar Ingila ba har rabuwarsa da Arsenal kafin zuwan Arsene Wenger da ya kawo sauyi.