✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitattun mutanen da aka yi garkuwa da su daga 2015 zuwa 2022

Wata garkuwa da aka yi da ta tayar da hankali, ’yan ta’addar sun sace Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru.

Duk da cewa Najeriya ta sha fama da wasu harkokin ta’addanci daban-daban, daga nesa ake jin labarin harkokin garkuwa da mutane domin kudin fansa.

Sai dai ko da lamarin ya iso Najeriya, ya fi kamari a Kudancin kasar nan a shekarun baya, kafin ya iso Arewa.

A watan Afrilun shekarar 2014 ne aka samu labarin ’yan Boko Haram sun yi garkuwa da dalibai mata a Makarantar Sakandaren Chibok da ke Jihar Borno, wanda ya jefa kasar nan a halin kaka-nika-yi.

Har yanzu akwai sauran daliban a hannun ’yan ta’addar bayan shekara 8, duk da cewa an samu nasarar kubutar da akasarinsu kuma a bana ma an kubutar da wasu.

A ranar Talata makon jiya ce aka yanke wa wanda ake ganin mai garkuwa da mutane mafi dukiya a Najeriya mai suna Chukwudumeme Onwuamadike da aka fi sani da Evans hukuncin daurin shekara 21, kari a kan daurin rai-da-rai da aka taba yanke masa a baya duk kan garkuwa da mutane.

An kama Evans ne a ranar 10 ga Yunin shekarar 2017 a katafaren gidansa da ke Layin Fred Shogboyede da ke yankin Magodo a Jihar Legas.

Daga wancan lokaci zuwa yanzu, harkar sace mutane ta zama ruwan dare a Najeriya, inda kusan ta karade yankin Arewa, inda babu wata jihar da ta tsira daga lamarin.

Matsalar wadda da farko ta fi shafar mutanen kauye, daga baya manyan ma ba su tsira ba.

Aminiya ta tattaro wasu fitattun mutane da aka yi garkuwa da su a kasar nan.

Shekarar 2015

A ranar 8 ga Afrilun 2014 ce aka yi garkuwa da Hakimin Wamakko, Alhaji Salihu Barade a garin Wamakko da ke Jihar Sakkwato.

Basaraken wanda dan uwan tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne, an sako shi ne bayan biyan fansar Naira miliyan 100.

Sai a ranar 2 ga Yunin shekarar aka kuma aka yi garkuwa da Gimbiya Oluwa Toyin Omosowon mai rike da Sarauniyar Akungba-Akoko da ke Jihar Ondo a lokacin.

An sako ta ce bayan biyan fansar Naira miliyan 20.

Garkuwa mafi girma a shekarar ita ce ta tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cif Olu Falae.

A ranar 21 ga Satumban shekarar ’yan bindiga suka farmakin gonar dattijon, da ke kauyen Ilado da ke Akure a Jihar Ondo, suka yi awon gaba da shi.

Daga baya sun sako shi bayan karbar fansar Naira miliyan 90, daga bisani an kama wasu da ake zargin da aika-aikar aka kai su kotu.

Haka kuma a ranar 14 ga Oktoba, an sace Cif Luckson Oberike, Babban Sarkin Biseni da ke Jihar Bayelsa, kafin ya kubuta bayan biyan fansar Naira miliyan 50.

Shekarar 2016

A ranar 5 ga Janairun shekarar 2016 ne aka yi wayi gari da sace Sarkin Obulu-Uku Igbodo, Obo Akaeze Ofolue da ke Jihar Edo.

Sace basaraken ya tayar da hazo bayan an zargi makiyaya da ta’asar. Sannan aka tsinci gawarsa bayan biyan kudin fansa na Naira miliyan 100.

A ranar 7 ga Afrilu, an sace fitaccen mawakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Dauda Kahutu Rarara a cikin garin Kano.

Sace mawakin ya karade kafofin sadarwa a lokacin, wanda bai rasa nasaba da alakarsa da Jam’iyyyar APC da kuma kasancewar a daidai lokacin ne harkar garkuwa da mutane ta fara kamari.

Garkuwar da ta fi tayar da hazo a shekarar, ita ce ta tsohuwar Minista, Laurentia Mallam da mijinta Mista Pius Mallam a hanyar Abuja zuwa Kaduna wadda aka yi a ranar 3 ga Oktoba.

An sako su ne bayan fansar Naira miliyan 10.

Shekarar 2017

A ranar 23 ga Mayun 2017, an yi garkuwa da Sarkin IbejuLekki da ke Jihar Legas mai suna, Baale Salino Kareem mai shekara 75.

An sako basaraken ne bayan biyan fansar Naira miliyan 20 a Legas.

Bayan mako guda wato ranar 30 ga Mayu, aka sace dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Takai/Sumaila, Alhaji Garba Umar Durbunde a hanyar Jere zuwa Bwari da ke tsakanin Kaduna da Abuja.

Shi ma an sako shi bayan biyan fansar Naira miliyan 10.

Shekarar 2018

A shekarar 2018 da ake tunkarar zaben 2019, an yi garkuwa da fitattun mutane da dama da ma talakawa.

Aminiya ta gano an kashe kusan Naira miliyan 700 a kudin fansar karbo wasu daga cikin mutanen da aka sace.

Daga cikin fitattun mutanen da aka sace, akwai Sarkin Ikulu, a Jihar Kaduna Mista Yohannah Kukah a ranar 3 ga Janairun 2018.

An sako basaraken bayan biyan kudin fansar Naira 100.

A ranar 26 ga Mayu, an sace tsohon Sanatan Abuja, Sanata Daniel Nyako, wanda Aminiya ba ta samu sahihin kudin fansar da ya biya ba.

Haka kuma a ranar 3 ga Yunin shekarar an sace Sarkin Ogobor da ke Jihar Delta, Mista Sunday Olisewokwu, wanda aka sako bayan biyan fansar Naira miliyan 200.

Sai kuma garkuwa da daliban makarantar Dapchi da aka yi a ranar 19 ga Fabrailun shekarar, inda ’yan Boko Haram suka farmaki makarantar, suka yi awon gaba da dalibai da dama a makarantar da ke Dapchi a Jihar Yobe.

Wannan garkuwar ce ta biyu irinta bayan ta Chibok da aka yi da daliban makaranta.

Shekarar 2019

Shekarar 2019 lokacin zabe ne, inda aka dan samu raguwar lamarin kadan a wasu wurare, wanda hakan ya sa wasu suke cewa akwai siyasa a cikin yaki da ta’addancin.

Duk da cewa a shekarar an samu raguwa, sai dai an yi garkuwa da Ministan Noma na yanzu, Dokta Muhammad Mahmood Abubakar, lokacin yana Shugaban Hukumar UBEC tare da ’yarsa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Garkuwa da Ministan ta tayar da kura matuka a lokaci, inda aka yi yada muryarsa ta waya lokacin yana hannun ’yan ta’addar.

Sai da aka biya fansar Naira mililyan 60 aka sako su.

Haka kuma a ranar 1 ga Mayun shekarar ce aka yi garkuwa da Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar wanda dan uwan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne a gaban gidansa da ke Daura a lokacin da yake shirin shiga Sallar Isha.

’Yan sandan Operation Puff Adder a karkashin jagorancin DCP Abba Kyari ne suka kubutar da shi a Kano bayan ya kwashe kwanaki a hannun masu garkuwar.

Shekarar 2020

A ranar Asabar 11 ga Yulin shekarar 2020 ce aka yi garkuwa da tsohon Sanatan Taraba ta Arewa, Sanata Zik Sunday a kauyen Bachama da ke Jihar Taraba.

An sako Sanatan ne bayan biyan fansar Naira miliyan 100.

A wani garkuwa da ya rikita kasar a shekarar, a safiyar Litinin, 23 ga Oktoban 2020 ’yan bindiga suka farmaki Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda suka sace Dokta Ibrahim Bako da matarsa da ’yarsa.

Lamarin ya tayar da kura sosai kasancewar farmaki ya kai ga zuwa cikin jami’a, da kuma ganin yadda ’yan ta’addar suka samu damar yin ta’asarsu suka fita lafiya.

Garkuwar ta zo ne bayan wasu makonni da sace wasu malamai a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Nuhu Bamalli mallakar Jihar Kaduna da ke Zariya.

An sako Dokta Ibrahim da iyalansa ne bayan biyan fansar Naira miliyan 10.

A watan Disamban 2020, an yi garkuwa da daliban Sakandaren Kankara da ke Jihar Katsina, inda ’yan ta’addar suka sace dalibai 303.

Sai dai an sako daliban daga baya, duk da cewa gwamnati ta ce ba ta biya kudin fansa ba.

Wanda ya shirya sace daliban, Auwalun Daudawa ya mika wuya daga baya, bayan ya yi sulhu da gwamnati, sannan daga baya ya koma daji, inda kwanaki kadan bayan komawarsa rikici ya barke a tsakaninsa da wata dabar ’yan ta’addar suka kashe shi.

A Nuwamba, ne kuma ’yan ta’adda suka kashe Alhaji Sagir Hamida, wanda ya taba neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna, sannan suka yi garkuwa da wasu mutane.

Sannan a ranar 19 ga Disamba, ’yan ta’addar sun sace daliban wata makarantar Islamiyya su 80 a Dandume na Jihar Katsina kwana biyu bayan na Kankara.

Sai dai jami’an tsaro sun nasarar kubutar da daliban a ranar.

Shekarar 2021

A wata garkuwa da aka yi da ta tayar da hankali, ’yan ta’addar suna sace Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 14 ga Satumban 2021.

An sako Sarkin Mai daraja ta Daya ne bayan ya kwashe kwanaki a hannun ’yan ta’addar, sannan an biya fansar Naira miliyan 10.

Sai a watan Disamba aka sace, Sarkin Gindiri a Jihar Filato, Cif Charles Mato Dakat, sannan aka sako shi bayan biyan fansar Naira 500,000.

Kuma a shekarar ce aka fi samun sace-sacen dalibai a makarantu daban-daban a fadin kasar nan.

A ranar 17 ga Fabrairu, ’yan bindiga sun sace mutum 41 ciki har da dalibai a Makarantar Kagara da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Sai kuma a 26 ga Fabrairu suka sace dalibai mata a makarantar mata ta Jangebe da ke Jihar Zamafara.

A ranar 11 ga Maris, ’yan ta’addar sun sace dalibai a Makarantar Koyon Aikin Noma da ke Afaka a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Wannan sace dalibai ya tayar da kura sosai domin an yi ta gudanar da zanga-zanga kafin aka rika kubutar da daliban kadan-kadan har aka kai ga kubutar da na karshe a watan Mayun shekarar.

Sai kuma a watan Afrilu, aka yi garkuwa da daliban Jami’ar Greenfield da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Cikin kwanaki kadan da garkuwar aka samu gawar dalibai uku cikin wadanda aka sace, wanda hakan ya jefa jihar a cikin jimami.

Lamarin ya yi zafi ne kasancewar Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ba za ta yi sulhu da ’yan binidga ba, ballantana ta biya su kudin fansa.

Bayan kwana 40, aka samu labarin sauran daliban sun dawo, inda iyayensu suka ce sun biya fansar Naira miliyan 150 da sababbin babura 8.

Sai a ranar 30 ga Mayu, aka sace wasu daliban makarantar Islamiyya a Jihar Neja.

Sai kuma ranar 17 ga Yuni, ’yan bindiga suka sace dalibai mata a makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Yawuri a Jihar Kebbi, inda har yanzu akwai sauran daliban a wajen ’yan ta’addar.

Daga cikin wadanda suka rage, akwai daliba mai suna Farida da ake rade-radin dan bindiga Dogo Gide ya aure ta, sannan ya aurar da sauran ga wasu.

Shekarar 2022

Daga cikin wadanda aka sace a bana akwai dan Ministan Sadarwa, Al’amin Isa Pantami a Bauchi, wanda aka sako daga baya.

Sai kuma ’yan bindiga da suka yi awon gaba da wani DPO na ’yan sanda da aka tura aiki Birnin Gwari a Jihar Kaduna wanda suka sace a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari yana kan hanyar tafiya don kama aiki, kuma har yanzu ba su sake shi ba.

‘Ana samun sauki’

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa ana samun sauki lamarin a Arewa bayan fatattakar ’yan ta’addar da jami’an tsaro suke yi.

A kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta ce zuwa watan Disamban bana za ta murkushe ’yan ta’addar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya ba da tabbacin hakan a jawabin hadin gwiwa kan tsaro da suka yi tare da Ministan Tsaro da na Harkokin ’Yan sanda.

Aregbesola ya ce: “Muna bai wa ’yan Najeriya tabbacin isasshen tsaro da aminci, shi ya sa Shugaban Kasa ya umarce mu da mu sanar da ku cewa daga yanzu zuwa watan Disamba, kullum tsaro da aminci da za ku samu za su inganta.

“Abin da muke fama da shi yanzu ba wani abu ba ne face harin matsorata da aka tarwatsa a maboyarsu a wurare da dama, wadanda suna yin haka ne don a rika ganin cewa har yanzu da sauran karfinsu.

“Babbar manufarmu ita ce kawar da su gaba daya sannan mu dawo da aminci a ko’ina a fadin kasar nan; kuma da izinin Allah hakan zai samu zuwa watan Disamban bana,” inji shi.

Aminiya ta ruwaito an samu sauki a wasu bangarori na jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Neja, yayin da wasu bangarorin kuma suke ci gaba da fama da matsalar.

Daga cikin yankunan da aka samu sauki a Kaduna, akwai yankin Birnin Gwari da ya sha fama da lamarin.

Dalilin da ake sace fitattun mutane —Masani

A hirarsa da Aminiya, masanin tsaro, Malam Kabiru Adamu, ya ce ana garkuwa da dalibai ne saboda ribar da ke tattare da garkuwa da su din inda gwamnati take barin daliban babu kariya a makarantu.

“A takaice dai ga riba ga babu kariya. Na uku kuma shi ne rashin horo. Duk lokacin da abubuwan nan uku suka faru za ka ga ana samun matsalar tsaro.

“Akan tattara daliban da yawansu a wuri guda inda babu tsaro mai inganci. Sannan bayan an sace su hankalin kasa yakan tashi a yi ta magana a kai.

“Wannan kan sa dole gwamnati ta shiga tattaunawa da su.

“Sannan bayan sace dalibai a Arewa maso Yamma da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya sai muka fahimci wata al’ada ta shigo wa ’yan ta’addar ta cewa duk wanda ya sace dalibai to ya gawurta za a ce ya yi fice.

To wannan sai ya zama kamar gasa a tsakaninsu ta yadda duk kungiyar da ba ta yi ba cikinsu ita ma za ta yi alwashin sai ta sace daliban domin a ce karanta ya kai tsaiko,’’ inji shi.

Kan dalilan da ke sa ake garkuwa da dalibai ya ce dalilai guda biyu ne galibi ke sa a yi garkuwa da mutanen watodon samun riba daga kudaden fansar da kuma dalilai na siyasa.

A cewarsa, daga dukkan bangarorin biyu fitattun mutane ne suke da kudin biyan fansar saboda su ke da damar tattalin arziki.

Sannan a bangaren siyasa kuwa dalilai na akida ko wata bukata da kungiyar ta’addancin ke da ita na ta kame wanda take bukata domin ta gabatar da bukatarta sakamakon fitattun mutane su ne idan aka kama su gwamnati za ta saurari ’yan ta’addar domin a shiga yarjejeniya da su.

Ya ce magance matsalar yana tattare da karfafawa da inganta tsaro da kariya da ake bai wa jama’a sannan ya bayyana abubuwa uku da ya ce a tsarin kimiyyar tsaro duk sa’ar da ake da matsala ta tsaro su ne ake dubawa.

Ya ce, “Na farko, me yake sa wanda yake aikata laifin yake aikata shi?’’

Ya kara da cewa, “Idan ka duba satar jama’a don karbar kudin fansa; akwai abubuwan da aka gano: Na daya akwai matsala ta zamantakewa a tsakanin Fulani da Hausawa da kuma jami’an tsaro.

“Akwai kuma batun shaye-shaye da rashin adalci a tsarin hukunta mai laifi. To lallai ne a magance dukkan wadannan don hana mai son ya aikata abin ya je ya yi.

“Na biyu, shi ne ribar da yake samu idan ya yi abin. Dole ne a samu hanyar na tsari na gwamnati na bibiyar kudade da hana hanyar da zai je ya samu kudaden.

“Na karshe, shi ne damar da zai je ya yi. Wato daga nan ana kallon wanda ake garkuwar da shi, wadanne matakai za a dauka don a kare shi a hana wanda zai je ya yi satar ya je ya yi.

“Sai kuma jami’an tsaro kan irin matakan kariyar da za su dauka domin koda wanda zai aikata laifin yana so ya aikata sai ya wahala. Sai an hada dukkan wadannan kafin a magance matsalar,’’ inji shi.

Dangane da batun bambancin kudin fansar da masu garkuwar ke karba daga yankin Kudu da Arewa kuwa, masanin ya danganta abin da bambancin yanayin zamantakewa na yankunan biyu.

“Yawanci masu garkuwa da mutane a Kudu suna da kungiyoyi ne masu tsari suna tsara abin da suke yi sannan suna da manufar da suke son cim mawa.

“Mai yiwuwa a cikin manufar nan suna da kudaden da suke muradin samu. Wannan ya sa suke sa kudade da yawa idan sun yi garkuwa da mutum duk da su ma a can suna da masu garkuwar da ba su da tsari.

“Ko Arewa ma idan manyan kungioyin ta’addanci suka yi garkuwa sukan bukaci manyan kudade. A takaice lamarin ba sashi ba ne yanayi kawai na kungiya,” inji masanin.