✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Fitaccen malamin Shi’a a Kaduna, Sheikh Badikko, ya rasu

Malamin ya rasu yana da shekara 59 a duniya

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma mabiyin mazhabar Shi’a a Kaduna, Sheikh Hamza Muhammad Lawal Badikko, ya rasu.

Malamin, wanda kuma shi ne Sakataren gidauniyar Thaqalayn Cultural Foundation, ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis, yana da shekara 59 a duniya.

An dai yi jana’zarsa ce a gidansa da ke unguwar Marafa a Kaduna, kafin daga bisani a binne shi makabartar titin Bashama Road.

Daya daga cikin daliban malamin, Yusuf Bala, wanda ya tabbatar wa Aminiya da rasuwar ya ce gabanin rasuwar Sheikh Badikko, lafiyarsa kalau.

Yusuf ya kuma bayyana marigayin a matsayin jagora na gari kuma abin koyi, wanda ya sadaukar da ilahirin rayuwarsa wajen karantar da ilimin Musulunci.

Marigayin ya rasu ya bar matarsa daya da ’ya’ya biyar.