A ranar Lahadi, 26 ga watan Disamban 2021, kungiyoyin kwallon kafa guda 18 da ke buga gasar Firimiyar Ingila aka tsara za su fafata a wasannin mako na 19.
Sai dai daga bisani an dage wasanni uku daga cikin wasanni 9 da za a fafata sakamakon harbuwa da cutar Coronavirus da wasu daga cikin ’yan wasan kungiyoyin suka yi.
- ’Yan sanda sun kama surukin Sanata Rochas Okorocha
- Ma’aurata sun sayar da jaririnsu kan Naira dubu 50
Daga cikin wasannin da aka dage akwai wanda Burnley za ta karbi bakuncin Everton, sai wanda Leeds United za ta kai wa Liverpool ziyara da kuma wanda Wolverhampton Wanderers za ta karbi bakuncin Watford.
A bangaren wasannin da aka buga kuma, Manchester City da ke zaman ta daya a teburin gasar Firimiyar Ingila ta bana a halin yanzu, ta yi wa Leicester City da ta je mata bakunta ruwan kwallaye a wasan da aka tashi 6-3.
Dan wasan tsakiya na City Kevin De Bruyne ne ya yi Leicester shigar wuri yayin da ya jefa kwallon farko a minti na 5 sai Riyadh Mahrez da ya jefa kwallonsa a bugun fenareti a minti na , yayin da İlkay Gündoğan ya jefa tasa kwallon a minti 21.
Dan wasan Ingila, Raheem Sterling shi ma ya sakada kwallon a bugun daga kai sai tsaron raga a minti na 25 yayin da kuma Aymeric Laporte ya jefa wa City kwallonta ta biyar minti na 69 sannan Sterling ya kara wata minti na 87.
James Maddison da ya jefa kwallo a minti na 55 da Ademola Lookman da kwallonsa a minti na 59 sai kuma kwallon da Kelechi Iheanacho ya jefa minti na 65 su ne suka dan share hawayen magoya bayansu a filin wasan na Etihad.
Ita kuwa Norwich City kashinta ta kwasa yayin da Arsenal ta lallasa ta da ci biyar ba ko daya a wasan da aka fafata a Carror Road.
’Yan wasan Gunners da suka yi bushasharsu wajen zira kwallaye sun hada da Bukayo Saka da ya jefa kwallon farko a minti na 6. Kieran Tierney ne ya jefa kwallo ta biyu a minti na 44 yayin da Bukayo Saka ya sake jefa wata kwallon a minti na 67.
Shi ma Alexandre Lacazette ya leka komar Norwichi yayin da ya jefa kwallonsa a minti na 84 a bugun daga kai sai mai tsaron rage wato bugun fenareti. Emile Smith Rowe ne ya rufe taro da kwallo cikon ta biyar da aka jefa a mintin karshe gab da za a tashi daga wasan.
Kwallaye uku rigis Tottenham ta jefa a ragar Crystal Palace bayan ta karbi bakuncinta faran-faran. Hakan ya sanya kungiyar ta koma ta hudu a teburin Firimiyar Ingila da maki 29.
Harry Kane da Lucas Moura da kuma Son Heung-Min ne suka jefa kwallo a ragar Crystal Palace wadda ta kasa mayar da martani, sai dai an bai wa dan wasanta, Wilfred Zaha katin kora daga filin wasan bayan ya karbi katin gargari har guda biyu.
Kiris ya rage a tashi canjaras a wasan da aka barje gumi tsakanin Westham United da kuma Southampton.
Southampton wadda ta je bakunta filin wasan Westham da ake kira London Stadium, ta jefa kwallaye uku yayin da ita kuwa wadda ta karbi bakuncin ta jefa kwallaye biyu.
Kwallayen da Mohamed Elyounoussi da James Ward-Prowse da kuma Jan Bednarek su ne suka bai wa Southampton maki ukun da ta samu a wasan. Sai dai Westham ta dan huce takaici da kwallayen da Michail Antonio da Said Benrahma suka jefa mata duk da cewa ba hakan ta so ba.
Ana iya cewa da kyar Chelsea ta kwaci kanta a filin wasa na Villa Park inda ta je wa Aston Villa bakunta a wasan da aka tashi 3-1.
Matsi ne ya sanya dan wasan bayan Chelsea, Reece James ya ci gida a minti na 28 da fara wasan, inda kuma daga bisani reshe ya juye da mujiya a yayin da Jorginho ya samu bugun fenareti har sau biyu a wasan kuma ya yi amfani da damarsa.
Tsohon dan wasan Inter Milan da Manchester United, Romelu Lukaku ne ya sanya Chelsea a gaban Aston Villa da kwallon da ya jefa a minti 56 wanda ya zama ana 2-1 kafin kwallo cikon ta ukun da Jorginho ya ci a minti karshe.
Akwai kuma wasan da aka fafata tsakanin Brighton Hove Albion da Brentford wanda da shi ne aka rufe wasannin na ranar Lahadi.
Brighton ta tsare mutuncin gidanta yayin da ta lallasa Brentford da ci 2-0 a filin wasa na The American Expree Community.
Leandro Trossard da Neal Maupay ne suka jefa mata kwallaye biyu a minti na 34 da kuma na 42 wanda hakan ya bata damar samun nasara a kan abokiyar karawarta.