✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiyar Ingila na bincikar City kan badakalar kudade

Muna maraba da sake duba wannan batu a cewar City.

Hukumar gasar Firimiyar Ingila na zargin Manchester City da bayar da bayanan da ba su dace ba game da kudadenta.

Ana zargin City ta bayar da bayanan karya na tsawon shekaru tara a lokacin da kungiyar ke kokarin kafa kanta, a matsayin mai karfi a fagen kwallon kafa na Ingila da Turai bayan da ta koma mallakin dangin Abu Dhabi.

Wannan zargi na zuwa ne a karshen wani bincike na shekaru hudu da fitacciyar kungiyar kwallon kafa ta duniya ta gudanar, sakamakon kwarmata sakonni da wasu takardu na kulob din daga jami’an City, wadanda mujallar Jamus Der Spiegel ta buga a watan Nuwamban 2018.

A ranar Litinin hukumar Firimiyar Ingila ta fitar da wata doguwar sanarwa da ke ba da cikakken bayani game da jerin laifuka kusan 80 da ake zargin City da keta dokokinta na kudi da ta yi daga 2009 zuwa 2018, na farkon kakar wasanni tara a karkashin ikon Abu Dhabi.

A waccan lokacin, kungiyar ta lashe kofunan Firimiya uku – a 2012, 2014 da 2018 – a cikin abin da ya zama lokaci mafi nasara a tarihin City na shekaru 143.

Kungiyar ta kuma zargi City da wasu laifuka 30 da suka shafi rashin bayar da hadin kai ga binciken tun watan Disambar 2018.

Kungiyar ta ce ta mika laifin ga wata hukuma mai zaman kanta kafin a fara sauraren karar cikin sirri.

A cikin wata sanarwa da City ta fitar, ta ce ta yi matukar mamakin wannan zargin, “musamman idan aka yi la’akari da dimbin almubazzaranci da cikakkun bayanai da aka samarwa da hukumar Firimiyar da su.

City ta ce “Muna maraba da sake duba wannan batu da wata hukuma mai zaman kanta ta, don yin la’akari da cikakkun shaidun da ba za su iya musantawa ba.”

“Saboda haka muna sa ran ganin an kawo karshen wannan al’amari gaba daya.”