✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiyar Ingila: Manchester City ta doke Chelsea

Manchester City na bin bayan Arsenal da maki 39 a teburin Gasar Firimiyar Ingila.

Mai rike da kambun Firimiyar Ingila, Manchester City ta doke Chelsea da ci daya mai ban haushi, inda ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Arsenal zuwa maki biyar.

Manchester City ta gaza tabuka komai a kashin farko na wasan, amma bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ta warwasa bayan Jack Grealish da Riyad Mahrez sun shiga filin wasan.

Mahrez ya zura kwallo daya tilo da ta raba gardama a wasan a minti na 63.

Chelsea na mataki na 10 a teburin gasar, duk da yawan makudan kudaden da take kashewa wajen sayen sabbin ’yan wasa.

Kungiyar na fama da rashin gwarazan ’yan wasanta; Mason Mount, Reece James, sai kuma Raheem Sterling da Pierre-Emerick Aubameyang da suka samu rauni a karawarsu da Manchester City.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ce ke jan ragamar teburin gasar da maki 44, sai Manchester City ke biye mata a matsayi na biyu da maki 39.