A shekaranjiya Laraba ce Firayi Ministan Kasar Armeniya, Nikol Pashinyan ya sanar da al’ummar kasar cewa zai sauka daga mukaminsa kafin a gudanar da zaben kasar a watan Disamba da ke tafe. Ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai.
Pashinyan, kafin ya zama Firayi Minista ya kasance jagoran adawa a kasar, inda ya yi nasarar hawa kujerar Firayi Minista a watan Mayu bayan an hambarar da Jam’iyyar Republican mai mulki, sakamakon zanga-zangar makonni da al’ummar kasar suka gudanar kan yadda cin hanci da rahsawa suka yi katutu a kasar.
Firayi Ministan dai dama tuni ya yi alkawarin gudanar da zaben ’yan majalisar kasar ba tare da jinkiri ba, lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki.
Mista Nikol Pashinyan mai shekara 43 tsohon dan jarida ne wanda ya mallaki kamfanin kansa a 1998, kuma daga bisani ya tsunduma harkokin siyasa har ya samu nasarar zama Fiayi Ministan Armeniya a ranar 8 ga watan Mayun bana.
A taba daure Mista Pashinyan na tsawon shekara guda bisa tuhumarsa da bata sunan Ministan Tsaron Kasar, Serzh Sargsyan a lokacin da yake editan jaridar Haykakan Zhamanak, lamarin da masu fashin baki kan harkokin siyasar kasar ke ganin ya kara masa farin jini.
Bayan fitowarsa daga kurkukun ne ya kafa karamar jam’iyyar siyasa ta adawa a shekarar 2007, inda ya samu nasarar shiga Majalisar Dokokin Kasar a 2008. Kuma bayan faduwar Shugaban Kasar da yake goya wa baya, Ter-Petrosyan, an sake daure Mista Pashinyan na tsawon shekara 7 a kurkuku, sakamakon zarginsa da shirya wata zanga-zanga a kasar wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 10.