Firaministocin kasashen Turai uku, Poland da Jamhuriyar Czech da kuma Sloveniya sun ziyarci Kyiv babban birnin Ukraine domin tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky da Firaministan kasar, Denys Shmyhal.
Sun ziyarci Kyiv ne a matsayin wakilan Tarayyar Turai kuma don su bayyana irin goyon bayan da tarayyar za ta ba Ukraine, kamar yadda shugaban Ma’aikatan Ofishin Firaministan Poland, Michal Dworczyk ya sanar.
- Hare-haren masu jihadi sun addabi gwamnatin soji a Burkina Faso
- Yadda aka kama fasto ya yi wa karamar yarinya fyade
Shugabannin uku sun yi tafiyar ta jirgin kasa ne tare da shugaban jam’iyya mai mulki ta Poland Jaroslaw Kaczynski.
A Talatar da ta gabata ce jirgin da shugabannin ke ciki ya kama hanya kuma bai yi wani dogon zango ba ya tsallaka kan iyakar Ukraine da Poland kan hanyarsa ta zuwa birnin Kyiv.
Dworczyk ya nanata cewa Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO ba za ta shiga cikin yakin ba amma za ta yi duk mai yiwuwa domin taimaka wa kasar kan mamayar da Rasha ke yi ma ta.
Gwamnatin Ukraine ta ayyana dokar hana fita na sao’i 35 a babban birin kasar yayin da dakarun Rasha ke ci gaba da barin wuta, duk da cewa shugaban kasar ya kirayi sojojin Rasha su mika wuya.
Yanzu haka kungiyoyin agaji na kokawa kan yadda dubban fararen hula ke rufe ba tare da abinci ba.