Mahukunta Masallatan Alfarma na Saudiyya, sun bai wa Firaiministan Pakistan Imran Khan, damar shiga dakin da aka binne Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW) a masallacinsa da ke birnin Madina.
Shafin mahukuntan mai suna Haramai Sharifain ne ya bayyana hakan tare da hotunan Firaiministan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
- Mutum 8 sun rasu, 5 sun jikkata a hanyar Minna-Katsina
- Kumbon China da aka yi harsashen faduwarsa a Abuja ya rikito a Tekun Indiya
An bude wa Firaiministan tare da matarsa dakin da kabarin Manzon Tsiran yake yayin da suka ziyarci masallacin a ranar Lahadi.
Kazalika, a cikin dakin ne kuma akwai kaburburan Sahabbai biyu mafi falala na Manzon suke, wato Sayyadina Abu Bakr bn Saddiq da kuma Umar bn Khaddab, aminci ya kara tabbata a gare su.
Ingatattun tarihi sun bayyana cewa, bayan wafatin Manzon Allah, an binne shi ne a dakin matarsa, Nana Aisha RA, inda ya yi jinyarsa ta ajali kamar yadda al’ada ta tanadar na binne duk wani Annabi a inda ya rasu.
Kazalika, an binne halifofin biyu na Manzon Allah a kusa da kabarinsa bayan sun nemi alfarmar hakan daga wurin Nana Aisha.