Ana fargaba cewa wata hajiyar Najeriya daga jihar Kwara ta kashe kanta a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kwara, ta sanar cewa hajiyar ta yi ajalin kanta ne ta hanyar fadowa daga saman rufin masaukibta da ke Madina.
Hukumar ta ce hajiyar itace mutum ta biyu cikin alhazan jihar da suka rasu a Madina a bana.
Ta kara da cewa wani alhajin jihar mai suna Saliu Mohammed, ya rasu sakamakon rashin lafiya a Madina.
- An sa ranar fara kwaso alhazan Najeriya daga Saudiyya
- Sallah: Ɗan majalisa ya raba raguna 3000 da 250m a Zamfara
Alhaji Saliyo ya rasu ne a yayin da ake jinyar shi a sashin kula da lafiya na wani asibitin gwamnati da ke Madina.
Hukumar alhaza ta cikin wata sanarwa cewa “wadannan abubuwa masu ban tausayi be, amma tana mika wuya ga kaddara da sanin Allah a cikin dukkan al’amura.”
A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Abdulsalam Abdulkadir ya fitar, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalansu, inda ya roki Allah Ya jikan wadanda suka rasu Ya kuma gafarta musu.