Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta koka kan yadda alhazan kasar ke ci gaba da safarar goro zuwa kasar Saudiyya.
Shugaban tawagar masu karbar baki na NAHCON a Madina, Labaran Abdullahi, ya ce shigo da goro na janyo musu kalubale, domin yana kawo tsaiko a tashoshin jiragen sama.
Labaran Abdullahi ya bayyana haka ne ga wasu zababbun ’yan jarida a Madina a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa hukumar ta bullo da sabbin tsare-tsare don tabbatar da kai maniyyata masaukansu cikin gaggawa daga filayen jiragen sama.
- Rukunin farko na maniyyatan Borno sun sauka a Madina
- An daure dan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda Fyade
Ya kara da cewa wata matsalar ita ce yadda wasu maniyyata ke ajiye fasfo dinsu a cikin jakunkuna bayan an yi musu izini a Najeriya.
“Wasu daga maniyyatan sun yi kuskure sun sanya fasfo dinsu a cikin manyan jakunkunansu a bisa kuskure, don haka bincike domin tabbatar da matsayinsu a na daukar lokaci”.