✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fira Ministar New Zealand, Jacinda Ardern, za ta sauka daga mukaminta

Ta ce bayan hidimta wa kasar tsawon shekara shida, tana bukatar hutu

Fira Ministar New Zealand, Jacinda Ardern ta sanar da cewa za ta sauka daga mukaminta ranar bakwai ga watan Fabrairu mai zuwa.

Sanarwar tata mai cike da ba-zata ta zo ne yayin taron manema labarai na farko da ta yi a 2023 ranar Alhamis.

Ta ce, “Na san wannan aikin yana da bukatu da yawa, ni kuma ba ni da wadannan abubuwan a yanzu. Shi ke nan kawai,” in ji ta.

“Mun yi iya bakin kokarinmu wajen hidimtawa, yanzu lokaci ya yi. Lokacin tafiyata ya yi.”

Ajiye aikin nata dai zai fara aiki ne da zarar an nada sabon Fira Minista.

Ranar Asabar mai zuwa ce dai ake sa ran jagororin jam’iyyar Labour mai mulkin kasar za su hadu domin zaben wanda zai maye gurbin nata.

An zabi Jacinda ne a shekarar 2017 lokacin tana da shekara 37 a duniya.

Bugu da kari, tana daya daga cikin shugabannin kasashe mafiya ƙarancin shekaru a duniya, kuma ta biyu da ta taɓa haihuwa lokacin da take rike da mukamin.

Fira Ministar mai barin gado ta kuma sanar da cewa a ranar 14 ga watan Oktoba mai zuwa za a gudanar da zabe a kasar. (NAN)